Peter Obi Ya Yi Magana Kan Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu, Ya Fadi Abinda Yakamata 'Yan Najeriya Su Yi
- Peter Obi ya yi magana kan shirin Shugaba Tinubu na raba tallafin N8,000 ga iyalai 12m har na tsawon wata shida
- Obi ya bayyana cewa tallafin N8,000 ya yi kaɗan ya rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suka samu kansu a ciki a dalilin tsige tallafin man fetur
- Sai dai, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa ya gayawa ƴan Najeriya cewa su shiga cikin tsarin domin samun tallafin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Gregory Obi, ya yi magana kan shirin gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na bayar da N8,000 ga iyalai 12m domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Peter Obi ya bayyana N8,000 da shugaban ƙasar yake shirin bayar wa a matsayin tallafi ta yi kaɗan ta rage halin matsin da cire tallafin man fetur ya haifar.
Obi ya bayyana cewa kusan kowane iyali a ƙasar nan suna jin raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin sannan kusan kowane iyaye suna da buƙatar N8,000 ɗin saboda tsananin talaucin da ya yi wa ƴan Najeriya katutu, cewar rahoton Nigerian Tribune.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli yayin da yake jawabi a wajen bikin yaye ɗaliban makarantar Pacesetters School na shekarar 2023 a birnin tarayya Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Peter Obi ya yi nuni da cewa ana jin jiki sosai a ƙasar nan
Ya ƙara da cewa malaman makarantar da ba a biyansu albashi mai kyau sannan su ke bin bashin albashi na watanni, suna daga cikin waɗanda ke jin wannan raɗaɗin.
A kalamansa:
"Na gayawa mutane na su samu hanyar shiga cikin wannan tallafin na N8,000 saboda kusan kowa yana buƙatarsa. Daga iyaye har malamai kowa yana buƙatar N8,000 ɗin nan."
Shehu Sani Ya Yi Magana Kan Bayar Da Tallafin N8,000
A wani labarin kuma, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi magana kan tallafin N8,000 da gwamnatin Tinubu za ta bayar ga ƴan Najeriya.
Tsohon Sanatan ya bayyana shirin bayar da tallafin a wani tsari na almajirantar da ƙasa, inda ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi addu'a kafin su karɓa.
Asali: Legit.ng