Matar Shahararran Dan Kasuwa, Dahiru Mangal, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Matar Shahararran Dan Kasuwa, Dahiru Mangal, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Matar fitaccen dan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal, ta riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli
  • Hajiya Aisha Daihuru Mangal ta rasu ne a yammacin ramar Asabar bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya
  • Za a yi jana'izar marigayiyar a Kifar Guga, da ke jihar Katsina a safiyar Lahadi, 13 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rahotanni sun kawo cewa Allah ya yi wa matar shahararran dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Hajiya Aisha Daihuru Mangal ta rasu ne a wani asibitin Abuja a yammacin ranar Asabar, 15 ga watan Yuli bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Hajiya Aisha Dahiru Mangal ta rasu
Matar Shahararran Dan Kasuwa, Dahiru Mangal, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Hoto: Alfijir Labarai
Asali: UGC

Wata majiya ta iyalin ta ce za a yi jana'izarta a mahaifar Mangal da ke yankin Kifar Guga, a garin Katsina da misalin karfe 11:00 na safiyar Lahadi, 16 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Za a rina: Fitacciyar jami'a ta zama ta 2 mafi nagarta a Najeriya, shugabanta ya magantu

Marigayiya Hajiya Aisha ta mutu ta bar mijinta, yara da kuma jikoki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban rashi na uku da ya doki dan kasuwar kenan a jere

Wannan shine babban rashi na uku da shahararran ke yi a jere a baya-bayan nan.

A bara ne Allah ya yi wa kaninsa wanda yake shugaban kamfani rasuwa, yayin da dansa ya rasu kafin rasuwar dan uwan nasa, rahoton PM News.

An yi jana'izar surukin Sarkin Musulmi da Sarkin Bichi a jihar Kano

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa an yi jana'izar Malam Imam Galadanci, wanda ya kasance suruki ga Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli a jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gawar Galadanci ya isa Kano daga birnin Landan a ranar Talata, 11 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak

Jarumar Nollywood, Cynthia Okereke, ta mutu

A wani labarin, Legit.ng ta rahoto a baya cewa fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya watau Nollywood, Cynthia Okereke, ta riga mu gidan gaskiya.

Abokin aikinta a masana'antar shirya fina-fanai, Joseph Okechukwu, shi ne ya sanar da labarin mutuwarta ranar Laraba (yau) 12 ga watan Yuli, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng