Sowore Ya Lissafa Buhari, Surukinsa, Sanatoci Da Gwamnoni a Matsayin Abokan Harkallar Emefiele
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya yi martani a kan tuhume-tuhumen da ake yi wa dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Sowore ya bayyana zarge-zargen a matsayin shirme da yaudara don ara wa masu rike da madafun iko a gwamnati lokaci
- Ya ce ainahin laifin da Emefiele ya aikata zai kai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, danginsa da surukansa kasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Dan rajin kare hakkin dan adam kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya dasa ayar tambaya kan yanayin yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ke tafiyar da lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
A wata wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli, Sowore ya yi martani a kan tuhume-tuhume biyu da gwmanatin tarayya ke yi wa Emefiele na mallakar makamai ba bisa ka'ida ba a gaban babbar kotun tarayya a Lagas.
Dan fafutukar ya bayyana cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefiele duk kokari ne na siyan lokaci ga mutanen da ya yi zargin hukumar DSS na karewa.
Sowore ya ambaci abokan harkallar Sowore
Ga wallafarsa a kasa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ga wadanda ba su da masaniya game da tsarin @OfficialDSSNG, rike @GodwinIemefiele ba shi da alaka da girman laifukan da ya aikata, shirin shine rike shi a madadin wadanda ke rike da madafun iko.
"Idan za a hukunta @GodwinIEmefiele a kan ainahin laifukan da ya aikata na kudi, yi wa tattalin arziki zagoin kasa, satar kudade da daukar nauyin ta'addanci da sauransu...zai je kasa tare da @MBuhari, da ahlinsa gaba daya, surukansa, mambobin majalisarsa, shugabannin @OfficialAPCNg da dama, gwamnonin jihohi, Sanatoci, manyan jami'an yan sanda da na sojoji da ma mutane a hukumomin @OfficialDSSNG, @officialEFCC da ma kungiyoyin farar hula”.
Sowore ya kuma yi zargin cewa daga cikin dabarun da DSS ke amfani da shi shine tattaunawa da Emefiele kafin sakinsa daga inda yake tsare.
Ya rubuta:
"Da yawa za su kai kasa. Yanzu haka, ana kan tattaunawa, wannan 'tuhumar rikewa' ne kawai kafin su sake shi!"
Lauya ya nemi a kama Buhari kan badakalar Emefiele
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani lauya ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Barista Kingdom Okere ne ya yi wannan kiran yayin wata hira a shirin kalaci na Arise TV a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng