Gwamnan APC Uzodimma Ya Kara Albashin Ma’aikatan Gwamnati da N10,000 Ana Tsaka da Wahala a Kasar Nan

Gwamnan APC Uzodimma Ya Kara Albashin Ma’aikatan Gwamnati da N10,000 Ana Tsaka da Wahala a Kasar Nan

  • Gwamnan jihar Imo ya gwangwaje ma'aikatan jiharsa bayan da ya tallafa da karin albashi mai tsoka
  • An ruwaito cewa, gwamnan ya kara N10,000 kan albashin ma'aikata don rage radadin cire tallafin mai
  • An zare tallafin man fetur a Najeriya tun bayan da aka rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya sanar da karin albashin da N10,000 ga ma’aikatan jihar domin rage radadin cire tallafin man fetur da aka yi a kasar nan.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Otal din Rockview da ke Owerri a ranar Asabar, The Nation ta ruwaito.

Idan baku manta ba, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur tun ranar farko da ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Abba Gida Gida Ya Caccaki Tinubu Kan Wata Matsala Daya Tak, Sun Raba Gari

Gwamnan Imo ya kara albashin ma'aikatan gwamnati
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo kenan | Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Tasirin cire tallafi da cece-kucen da 'yan Najeriya ke yi

Wannan ya jawo cece-kuce a Najeriya, inda wasu ke ganin hakan zai taimaki tattalin arziki, wasu kuma za su sha wahala ne kawai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zuwa yanzu, ana ta kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta mayar da tallafin ko kuma ta kawo hanyar karin albashi.

A bangare guda, gwamnatin Tinubu ta ce za ta raba wa 'yan Najeriya miliyan 12 kudin da bai gaza N8000 a kowane wata don rage radadin.

Duk da haka, ana kallon gwamnatin da kokarin kakaba wa 'yan kasa wahalar da ba za su iya dauka ba.

Wasu masana sun jima da bayyana cewa, tallafin mai a Najeriya ba zai ci gaba da haifar da da mai ido ba duba da yadda wasu tsiraru ke amfani da tsarin a madadin 'yan kasar da suka dace kuma suka cancanta.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Martanin 'Yan Najeriya Kan Aniyar Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m

Gwamnan APC ya kara wa ma'aikatan jiharsa albashi, zai dauki sabbi sama da 1,000

A wani labarin, gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da karin albashin naira N10,000 ga kowane ma'aikacin jiha ba tare da la'akari da matakin aiki ba.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kai na jihar, Jude Okpor, ne ya bayyana haka ga manema labarin yayin da yake karin haske kan abinda aka tattauna a taron majalisar zartarwa.

Mista Okpor ya kuma bayyana cewa gwamnan ya aminta da kara daukar sabbin ma'aikata 1,454 a fadin kananan hukumomin jihar da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.