Bidiyon Mark Angel Mai Bidiyon Barkwanci Ya Bar Jama’a Baki Bude, Ashe Ya Iya Kwalliya
- Mark Angel ne ake yiwa kallo a matsayin daya daga cikin wadanda suka fara kirkirar bidiyon barkwanci a Najeriya, ya fara tun 2013
- Mark, wanda ya shahara da killace rayuwarsa a sirrance, kwanan nan ya yada wani faifan bidiyo na yadda ya taimaka wa wata mata ta fito daga mota mai tsafi, wacce ake kyautata zaton tasa ce
- A maganarsa ta baya-bayan nan, Mark ya kuma yada bidiyonsa a cikin mota yayin da ya bayyana dalilin da ya sa ba ya son tuka kasan a duk lokacin da yake cikin Legas
Daya daga cikin mashahuran masu barkwanci a Najeriya Mark Angel ya haifar da cece-kuce a kan wani faifan bidiyo da ya dauka a lokacin da aka gan shi yana taimakon wata mata lokacin da take fitowa daga mota mai zafi da ake zaton tasa ce.
“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo
Mark Angel, wanda aka san shi da wasannin ban dariya a shafukansa na yanar gida, ya cika mabiyansa da mamaki yayin da suka gay a sanya wasa sutura masu tsadar gaske.
Mark dai sananne da ‘yan tawagarsa, irinsu Emmanuela da Success, wadanda suka dade suna ba ‘yan Najeriya dariya.
Ya nufi kofar fasinja, inda ya bude wa matar kofa, su biyun suke tafiya cikin kwalisa da daukar hankali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kalli bidiyon:
A wani bidiyon na daban kuma, Mark ya ce bai son tuka mota a duk lokacin da yake cikin birnin Legas.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a bayan ganin bidiyon
blossom4forever:
“Wannan sokon namu Mark hadadde ashe wancan wandon da yake saka wa yake zuwa har ciki ke ruda mu.”
mcshemcomedian:
“Mai kudin boye kenan.”
ajebodcomedian:
“Tafiyar attajirai.”
swinnybae:
“Kenan @markangelcomedy zai iya saka tura ya yi kyau haka?”
leechi.ga:
“Buhun kudi, daya daga cikin fitattu, ka mai da barkwanci abin sha’awa.”
A karon farko, Buhari ya yi martani kan ce masa da ake 'Jubril na Sudan'
A wani labarin, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai jin dadin yadda ake barkwanci a kansa ta hanyar kiransa da 'Jurbil na Sudan'.
A cewar Buhari wannan fade da mutane ke yi ba abin dariya bane, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Buhari ya bayyana hakan ne a daren Juma'a 23 ga watan Disamba, yayin bikin karrada shugaba mai kishin kasa da iyalansa suka shirya a bikin cikarsa shekaru 80.
Asali: Legit.ng