Kotu Ta Umarci Hukumar PCACC Ta Saki Tsohon Kwamishinan Ganduje Da Ta Tsare
- Wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin a saki tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano daga tsare shin da ake yi
- Kotun ta bayar da umarnin ne bayan tsohon kwamishinan ya shigar da ƙara a gabanta inda ya buƙaci da a sake shi
- Ana zargin Malam Idrsi Wada Saleh da laifin yin sama da faɗi da N1bn na kuɗin gyaran wasu tituna a birnin Kano
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin Kano, a ranar Juma'a ta bayar da umarnin sakin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Malam Idris Wada-Saleh, daga kamun da aka yi masa har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar.
A ranar 4 ga watan Yuli hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da rashawa ta jihar (PCACC) ta gurfanar da Wada a gaban kotun majistare bisa zargin ba da bayanan ƙarya da cin amana, cewar rahoton PM News.
Hukumar ta bayyana cewa a cikin shekarar 2023 wanda ake ƙarar ya fitar da N1bn ga kamfanunnikan Arafat construction company, No stone construction company da Multi resources domin gyaran tituna 30 a cikin birnin Kano, amma ba a gyara ko ɗaya ba.
Sai dai, tsohon kwamishinan ya shigar da ƙara ta hannun lauyansa, Abdulgafar Murtala, a ranar 11 ga watan Yuli inda ya buƙaci kotun da ta hana hukumar ci gaba da tsare shi ko hantararsa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da hukumar PCACC, majistare Tijjani Sale-Minjibir, Muhyi Magaji Rimingado, gwamnatin jihar Kano, kwamishinan ƴan sandan jihar, hukumar DSS da hukumar Sibil Difens.
Alkalin kotun ya umarci da a saki tsohon kwamishinan
Mai shari'a S. A. Amobeda, ya amince da buƙatar da wanda ya shigar da ƙarar ya nema, inda ya umarci waɗanda ake ƙarar na farko zuwa na uku da su saki tsohon kwamishinan daga tsare shin da suka yi.
Gwamnan PDP Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Yadda Jiharsa Ke Asarar Biliyan N10 Duk Ranar Litini Saboda Abu 1
Ya kuma umarci waɗanda ake ƙarar da kada su sake cafkewa, tsarewa ko hantarar wanda yake ƙarar.
Alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 19 ga watan Yuli.
An Cafke Kwamishinan Ganduje
A baya rahoto ya zo cewa, hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, ta yi caraf da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar a gwamnatin Ganduje.
Hukumar ta cafke Malam Idris Wada Saleh tare da wasu mutum biyar bisa zargin yin sama da faɗi da N1bn na gyaran tituna.
Asali: Legit.ng