Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Rashin Lafiyar Gwamnan Jihar Ondo, Ta Bayyana Lokacin Da Zai Dawo Gida

Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Rashin Lafiyar Gwamnan Jihar Ondo, Ta Bayyana Lokacin Da Zai Dawo Gida

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi magana kan halin rashin lafiyar da gwamnan jihar Ondo ke ciki
  • Sakataren jam'iyyar na ƙasa ya bayyana cewa nan bada daɗewa ba gwamna Akeredolu zai dawo ya ci gaba da mulki
  • Jam'iyyar ta yi ƙarin haske kan kalaman da shugabanta na ƙasa ya yi kan rashin lafiyar gwamnan wanda yake jinya a ƙasar waje

Jihar Ondo - Sakataren jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya nuna ƙwarin guiwarsa kan cewa nan bada daɗewa ba gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu zai dawo ya ci gaba da jan ragamar jihar.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa Omisore ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a lokacin da ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar a birnin Akure babban birnin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Dirama: Wani Shaida da PDP Ta Gabatar Ya Bata Kunya a Gaban Kotu, Ya Bayyana Gaskiya

APC ta yi magana kan rashin lafiyar gwamna Akeredolu
Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akankunrin Akeredolu Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Omisore ya bayyana cewa babu bukatar a ɗaga hankula kan rashin lafiyar gwamnan inda ya yi nuni da cewa gwamnan hutu kawai yake buƙata.

A lokacin ziyarar, sakataren na jam'iyyar APC ya gana da manyan ƙusoshin jihar da suka haɗa da muƙaddashin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, shugaban jam'iyyar APC na jihar, kwamishinoni, mambobin majalisar dokokin jihar da sauran manyan ƙusoshin gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a fahimci kalaman Abdullahi Adamu ba kan rashin lafiyar Akeredolu, cewar Omisore

Omisore ya yi ƙarin haske cewa addu'ar da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi wa gwamman ba a fahimce ta da kyau ba ne.

Ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar bai taɓa cewa gwamnan ya koma bai iya taɓuka komai ba inda ya koka kan yadda wasu kafafen sadarwa suka sauya ainihin maganar shugaban jam'iyyar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnan APC Ya Ƙara Wa Ma'aikatan Jiharsa Albashi, Zai Ɗauki Sabbi Sama da 1,000

A kalamannsa:

Shugaban jam'iyya kawai ya buƙaci al'ummar Ondo su yi addu'ar samun lafiyar gwamnan ne, ba wai batun cewa ya koma bai iya taɓuka komai ba. Wannan ziyarar ta mu, mun yi ta ne domin ƙara jaddada matsayar uwar jam'iyya cewa muna addu'ar samun lafiyar gwamna Rotimi Arakunrin Akeredolu, ba wani abu daban ba."

Omisore a yayin ziyarar ya samu rakiyar mataimakin sakataren jam'iyyar na ƙasa, Mr Festus Fuanter, mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa (yankin Arewa ta Tsakiya), Hon. Bawa Muazu, da mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa (yankin Kudu maso Yamma), Hon. Isaacs Kekemeke.

Gwamnan Ondo Ya Kara Wa'adin Neman Magani a Kasar Waje

A baya rahoto ya zo gwamnan jihar Ondo ya ƙara wa'adin neman maganin da ya tafi yi a ƙasar waje saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.

Gwamna Akeredolu ya ƙara wa'adin zuwa har sai baba ta gani a wata wasiƙa da ya aikewa da majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng