Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Zamfara

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Zamfara

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ceto mutum tara da ƴan bindiga suka sace a wani bata kashi da suka yi da su a jihar Zamfara
  • Dakarun sojojin sun ceto mutanen ne a ƙaramar hukumar Bukkuyum bayan sun yi gumurzu da ƴaa bindigan
  • Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin sati ɗaya da dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' ke ceto mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' a ranar Juma'a sun ceto mutim tara da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun ceto mutanen ne a ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara bayan sun yi bata kashi da ƴan bindigan.

Dakarun sojoji sun ceto mutum tara a jihar Zamfara
Wasu dakarun sojoji a jihar Zamfara Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Jaridar Channels tv ta tattaro cewa dakarun sojojin a yayin da su ke gudanar da sintiri da ba manoma kariya a gonakinsu, sun samu kiran gaggawa kan zuwa ƴan bindiga ƙauyen Mailere a yankin Gwashi na ƙaramar hukumar ta Bukkuyum.

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Yi Awon Gaba Da Wata Likita Bayan Yin Basaja A Matsayin Marasa Lafiya

Dakarun sojojin sun fatattaki ƴan bindigan

Wani babban majiya daga ɓangaren sojojin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa dakarun sojojin sun isa ƙauyen da gaggawa inda suka yi kaciɓus da ƴan bindigan a ƙofar shiga ƙauyen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai dakarun sojojin sun yi musanyar wuta da ƴan bindigan inda suka fatattake su da tilasta su barin mutum taran da suka sace.

Tuni dai har an miƙa mutanen da lamarin ya ritsa da su a hannun iyalansu.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin sati ɗaya da dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadarin Daji' suka ceto mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su, cewar rahoton TVC News.

A cikin ƴan kwanakin nan dakarun sojoji sun ƙara matsa ƙaimi wajen fatattakar ƴan bindiga a jihar Zamfara, wacce ta daɗe tana fama da matsalar ayyukan ta'addancin ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Jam'iyyar APC Da Aka Sace Ya Kubuta Daga Hannun 'Yan Bindiga, An Cafke Wadanda Ake Zargi Da Sace Shi

Dakarun sojojin na ci gaba da fatattakar ƴan bindigan ne biyo bayan shugabannin sojojin sun bayyana cewa ba batun yin sulhu da ƴan bindiga da suka daɗe suna addabar mutanen jihar Zamfara.

Sojoji Sun Ceto Mutum 30 a Hannun 'Yan Bindiga

A wani labarin na daban kuma, dakarun sojoji sun ceto mutum 30 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kebbi.

Dakarun sojojin sun ceto mutanen ne bayan sun yi bata kashi da miyagun ƴan bindigan a cikin jeji. Mutanen da aka ceto ɗin sun fito daga jihohi uku masu makwabtaka da jihar Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng