Yanzu Yanzu: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Yi Hatsari a Benue

Yanzu Yanzu: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Yi Hatsari a Benue

  • Mummunan al’amari ya faru da rundunar sojin Najeriya yayin da jirginta ya yi hatsari a Makudi, babban birnin jihar Benue
  • Daraktan hulda da jama’a na rundunar NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da abun bakin cikin
  • A cewar Gabkwat, lamarin ya afku ne ranar Juma’a, 14 ga watan Yuli, lokacin wani atisaye kuma matukan jirgin sama biyu ne a ciki yayin da hatsarin ya afku

Benue - Wani jirgin saman horar da sojojin saman Najeriya FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Channels TV ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli, yayin wani atisaye.

Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Benue
Yanzu Yanzu: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Yi Hatsari a Benue Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Daraktan hulda da jama'a da labarai na rundunar NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya sani a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yan Sandan Jigawa Sun Kama Likitan Bogi Da Ya Dade Yana Cutar Da Al'umma

Matuka biyu da ke cikin jirgin sun tsira kuma suna asibitin sojoji, inji kakakin rundunar NAF

Ya ce matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira kuma ana kan kula da su a wani asibitin sojoji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gabkwet ya ce:

"An yi sa'a matukan jirgin biyu sun tsira a hatsarin bayan da suka yi nasarar fita daga jirgin. Bugu da kari, ba a rasa rai ko daya ko lalata kaya a yankin da abun ya faru ba.
"Yanzu haka dukka matukan jirgin na karkashin kulawa a asibitin sojoji, Makurdi. A halin da ake ciki, shugaban hafsan soji, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya kafa wani kwamitin bincike don gano abun da ya haddasa hatsarin."

"Babu maganar sulhu": Rundunar sojoji ta yi gargadi ga yan bindiga

A wani labarin kuma, rundunar sojin ƙasan Najeriya ta yi kira ga 'yan ta'adda da 'yan bindigan jeji musamman a shiyyar Arewa maso Yamma su gaggauta miƙa wuya tun da wuri.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Yi Ram Da Sojan Bogi Da Ya Dade Yana Kwacen Kudaden Al’umma

Rundunar sojin ta jaddada cewa ba bu zancen zama teburin sulhu da gurɓatattun mutanen da su ka zama barazana ga zaman lafiya a ƙasar nan.

Babban kwamandan rundunar sojin sashi na 8 a hukumar soji, Manjo Janar Godwin Mutkut ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Gusau, babban birnin Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng