Babbar Kotun Tarayya Ta Ba DSS Umarnin Sakin Emefiele Cikin Gaggawa

Babbar Kotun Tarayya Ta Ba DSS Umarnin Sakin Emefiele Cikin Gaggawa

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba jami’an hukumar DSS umarnin sakin Emefiele cikin gaggawa
  • Kotun ta bayana cewa kama Emefiele da tsare shi gami da tuhumarsa da DSS ta yi a matsayin haramtaccen abu
  • Kotun ta kuma soke duk wani sammaci na kamun Emefiele da kuma haramtawa duk wasu hukumomi sake kama shi

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayyana kama Godwin Emefiele da tsare shi da jami'an tsaro na farin kaya suka yi, a matsayin haramtacce tare ba da umarnin a sake shi ba tare da ɓata lokaci ba.

Mai shari’a Bello Kawu ya bayyana cewa, tsare Emefiele da ci gaba da yi masa tambayoyi ya saɓawa hukuncin da aka yanke da kuma umarnin mai shari’a M. A. Hassan kamar yadda PM News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru 10 Ba Miji, 'Yar Najeriya Ta Sace Zuciyar Santalelen Bature, Ana Gab Da Aurensu Yanzu

Emefiele ta bakin lauyansa, Peter Abang, ya roƙi kotun da ta jingine tuhumar da DSS ke masa saboda ta saɓa doka sakamakon hukuncin da wata kotu ta yanke a ranar 29 ga watan Disamban 2022.

Kotu ta umarci DSS ta saki Emefiele
Babbar kotun tarayya umarci DSS ta saki Emefiele cikin gaggawa. Hoto: @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu ta haramtawa hukumomi sake kama Emefiele

A ci gaba da yanke hukunci, mai shari’a Kawu ya kuma bayar da umarnin yin watsi da duk wani sammacin kama Emefiele da wata hukuma ta samu a baya.

DSS na zargin Emefiele da daukar nauyin ta’addanci, zamba cikin aminci, halasta kudaden haram, da kuma barazana ga tsaron kasa.

Kotun ta kuma ba da umarnin hana hukumar DSS kama, tsare, ko yin kutse ga ‘yancin kai na Emefiele ko kuma tauye masa ‘yancin zuwa inda ya ga dama.

Daga karshe, kotun ta bayar da umarni ga hukumar DSS da su gaggauta sakin Emefiele, sannan ta hana hukumar kama shi a gaba.

Kara karanta wannan

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

Lauyan Emefiele ya yabawa alkalan Najeriya

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kamala shari’ar, lauyan Godwin Emefiele ya jinjinawa alkalan Najeriya, wadanda ya ce ba sa tsoron yin hukunci na adalci duk da barazanar da jami’an tsaro suke musu.

Ya ce hakan wani abu ne da ya kamata ‘yan Najeriya su yi farin ciki da shi, saboda a cewarsa alkalan ba sa la’akari da wanda yake kara ko ake kararsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa lauyan na tsohon gwamnan babban bankin, ya bukaci jami’an na DSS da su yi kokarin bin umarnin kotu domin bai wa wanda yake karewa damar zuwa a duba lafiyarsa

An kama wani likita na bogi a jihar Jigawa

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan kama wani likitan bogi da jami'an 'yan sanda suka yi a Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Wanda aka kama mai suna Samuel David, ya kwashe tsawon lokaci yana duba marasa lafiya ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng