Miyagun Yan Bindiga Sun Halaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Delta

Miyagun Yan Bindiga Sun Halaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Delta

  • Tsagerun 'yan bindiga sun yi ajalin Insufektan 'yan sanda a shingen bincike a yankin karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta
  • Lamarin ya faru ranar Laraba da yamma lokacin mamacin da abokan aikinsa na zaune a cikin mota, sauran sun tsira da rayuwarsu
  • Bayanai sun nuna wannan kisa na zuwa ne watanni biyu bayan wasu mahara su halaka yan sanda da dama a Ughelli

Delta - Miyagun 'yan bindiga sun halaka ɗan sanda wanda ya kai matsayin Insufekta a yankin Ughelli, ƙaramar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta ranar Laraba da yamma.

Wannan harin na zuwa ne watanni biyu bayan halaka wasu jami'an hukumar 'yan sanda a garin Ughelli, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Harin yan bindiga kan yan sanda.
Miyagun Yan Bindiga Sun Halaka Insufektan Yan Sanda a Jihar Delta Hoto: leadership
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa mamacin mai suna Insufekta Jude Ukpaka na cikin motar 'yan sanda tare abokan aikinsa lokacin da maharan suka farmake su a shingen bincike da ke kan titin Ogor-Evwreni-Ughelli.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika, An Kama Wani Mai Hannu a Kazamin Harin da Aka Kai Wa Babban Malami a Najeriya

Yadda lamarin ya faru

Maharan sun bindige ɗan sandan, wanda ke aiki a tawagar sintirin Dragon 19 Security da ke Ughelli kuma suka yi awon gaba da bindigarsa ƙirar AK47.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran jami'an yan sandan da ke tare da mamaci a lokacin da maharan suka buɗe musu wuta, sun yi nasarar tserewa zuwa cikin gonakin da ke kusa da wurin.

A ruwayar Vanguard, Wata majiya ta ce:

"Sauran guduwa suka yi cikin fadamar gonaki har sai da tawagar dakarun yan sanda daga ofishin Ughelli suka kawo ɗauki suka cece su. Gawar Insufektan da aka kashe kuma an kaita ɗakin aje gawarwaki."

An tattaro cewa wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙaruwar aikata muggan laifuka da ta'addancin 'yan ƙungiyoyin asiri a Ughelli da kewaye.

Yayin da aka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, don tabbatar wa bai ce komai game da kisan insufektan ba.

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima

A wani rahoton na daban kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana tushen abinda ya haifar da yan bindiga a arewacin Najeriya.

Ahmad Sani Yerima, ya yi ikirarin cewa talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta'addancin 'yan bindigan jeji a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262