Gini Ya Danne Shugaban Alkalan Jihar Ekiti a Ofishinsa, Yana Kwanta a Asibiti

Gini Ya Danne Shugaban Alkalan Jihar Ekiti a Ofishinsa, Yana Kwanta a Asibiti

  • Shugaban alkalan jihar Ekiti, Mai shari'a Oyewole Adeyeye, ya tsallake rijiya da baya yayin da gini ya rufta kansa ranar Laraba
  • Rahoto ya nuna cewa Alkalin na cikin ofishinsa gabanin tashi daga aiki ba zato wani sashin ginin babbar Kotun jiha ya ruguje ya danne shi
  • A halin yanzun yana karkashin kulawar likitoci a Asibitin da ba'a ambaci sunansa ba a cikin jihar Ekiti

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ekiti- Shugaban alkalan jihar Ekiti, mai shari'a Oyewole Adeyeye, ya tsallake rijiya da baya ranar Laraba lokacin da wani sashin ginin babbar kotun jiha ya kife kansa a Ofis.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne yayin da shugaban alkalan ke cikin Ofishinsa a ginin babbar Kotun Ekiti ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, 2023.

Babban Jojin jihar Ekiti, Oyewole Adeyeye.
Gini Ya Danne Shugaban Alkalan Jihar Ekiti a Ofishinsa, Yana Kwanta a Asibiti Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna a halin yanzu Mai shari'a Oyewole Adeyeye na kwance a Asibiti karkashin kulawar likitoci a wani Asibiti da ba'a bayyana ba a cikin jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Kuma Dai: Tinubu Ya Nemi Majalisa Ta Amince Masa Ciyo Bashin Dala Miliyan 800 Daga Bankin Duniya, Ya Sanar Da Abin Da Zai Yi Da Kudin

An ce lamarin ya faru da yamma ana dab da tashi aikin ranar Laraba kuma shugaban alkalan na cikin ofishinsa lokacin da wani sashin ginin ya rushe ya danne shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan kuma ana tsammanin rushewar ginin ba zai rasa nasaba da rashin ƙarkon ginin ba sakamakon mamakon ruwan sama da ake sha a jihar, kamar yadda The Eagle ta ruwaito.

Mutum nawa ibtila'in ya shafa?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ba'a rasa rayuwar ko mutum ɗaya ba sanadiyar rugujewar ginin amma shugaban alkalan ya samu raunuka saboda katangar ginin ofishinsa ta faɗo kansa.

Sai da ma'aikata suka zage dantse suka yi aikin ceto dagaske kafin daga bisani suka ci nasarar zaƙulo mai shari'a Oyewole Adeyeye daga cikin ɓaraguzan ginin.

Duk wani yunkurin neman jin ta bakin rijistaran babbar Kotun jihar domin samun cikakken bayani bai kai ga nasara ba domin ya turo sakon cewa ba zai saurari yan jarida ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Jihar Zamfara Ta 'Talauce', In Ji Gwamna Lawal Dare

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan samar da Abinci a Najeriya

A wani rahoton na daban Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu , ya ayyana ta ɓaci kan samar da isassen abinci a Najeriya.

Ya kuma bada umarnin a gaggauta buɗe rumbun gwamnati, a fito takin zamani da hatsi a rabawa manoma da magidanta a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262