An Gano Gawar 'Dan Sanda Na Musamman' Cikin Yan Bindiga Da Sojoji Suka Sheke A Filato
- Rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau ta hallaka ‘yan bindiga uku da suka addabi jama'a
- An tura rundunar karamar hukumar ne don maido da zaman lafiya tare da dakile hare-haren 'yan bindiga a yankin
- Burgediya Janar Onyema Nwachukwu, daraktan hulda da jama’a na hukumar shi ya bayyana haka a jiya Laraba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Plateau – Rundunar sojin Najeriya ta hallaka ‘yan bindiga uku a karamar hukumar Mangu da ke jihar Plateau.
An tura rundunar yanki na ukun ne karamar hukumar don dakile hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu shi ya bayyana haka a wata sanarwa ta kafar Twitter.
Rundunar ta fadi yadda jami'ansu suka hallaka 'yan bindigan
Ya ce an gudanar da samamen ne a jiya Laraba 13 ga watan Yuli bayan samun kiran gaggawa daga jama'an yankin karamar hukumar Mangu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Samun kiran ke da wuya rundunar ta isa wurin inda ta yi ajalin ‘yan bindiga uku bayan artabu da su.
Ya ce bayan ‘yan bindigan sun tsere daga dajin, rundunar ta samu muggan makamai da wasu abubuwa da tsageran suka bari.
Jihar Plateau na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankin karamar hukumar Mangu.
Ya ce rundunar ta bazama neman sauran 'yan bindiga
A cewar sanarwar:
“Rundunar mu ta kwato muggan makamai da suka hada da AK-47 guda uku da alburusai da dama sai kuma babur guda daya da katin shaidar aikin jami’an ‘yan sandan sa kai.”
Nwachukwu ya kara da cewa rundunar tasu ta bazama cikin daji neman sauran ‘yan bindigan da suka tsere.
Mafi yawa daga cikinsu sun tsere ne da alburusai a jikinsu yayin artabu da rundunar sojojin a jihar, cewar Daily Post.
Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga 3 a Jihar Plateau
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta hallaka 'yan bindiga uku a karamar hukumar Mangu a jihar Plateau.
Rundunar sun yi arangama da tsageran kafin samun nasara a kansu a kan hanyar Mangu zuwa Pushit da ke jihar.
Dalilin fafatawar, jami'an sojin sun yi nasarar kwatar muggan makamai a hannun 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng