Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kai Wa Ayarin Babban Malami Hari
- Dakarun yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargi da hannu a harin da aka kai wa fitaccen malamin coci, Apostle Johnson Suleman
- Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan kasar nan, Muyiwa Adejobi, ya ce jami'ai sun kwato manyan bindigu daga hannunsa
- Mutumin mai suna Yusuf Isah ya shiga hannun jami'an yan sanda na sashin tattara bayanan sirri bayan gudanar da bincike mai zurfi
FCT Abuja - Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kama wani mutumi ɗan shekara 32 a duniya mai suna, Yusuf Isah, bisa zargin yana da hannu a harin da aka kai wa babban Malamin coci.
Jaridar Punch ta rahoto cewa mutumin ya shiga hannu ne kan zargin alaƙa da kazamin harin da aka kai wa babban Fasto kuma shugaban mabiya Omega Fire Ministries na duniya, Johnson Suleman.
Yadda mummunan harin ya faru
Idan baku manta ba a watan Oktoba, 2022, wasu miyagun 'yan bindiga suka farmaki ayarin motocin fitaccen Faston a kan titin Benin-Auchi cikin jihar Edo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin wannan hari, 'yan bindigan sun halaka mutane shida kuma daga cikinsu harda jami'an hukumar 'yan sanda guda uku.
Yadda muka kama wanda ake zargi - hukumar 'yan sanda
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya tabbatar da kama Yusuf Isa ga 'yan jarida a birnin tarayya Abuja.
Da yake jawabi yayin nuna wanda ake zargin, Adejobi ya ce jami'an sashin tattara bayanan sirri (FIB-IRT) ne suka kama Isah bayan gudanar da bincike mai zurfi.
Ya ce yan sanda sun kwato bindigun AK-47 guda 5, bindigun K2 guda biyu da alburusai 180 daga hannun wanda ake zargi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
"Bayan bincike mai zurfi dangane da harin da aka kai wa ayarin Fasto, Apostle Johnson Suleman, jami'an sashin FIB-IRT sun kama Yusuf Isah ɗan asalin garin Okene, jihar Kogi kuma yana sana'a a Akure, jihar Ondo."
"An samun bindigun Ak47 guda biyar, bindiga ƙirar K2 guda biyu, alburusai guda 180 da kuma wasu abubuwan fashewa 4 a gidan da yake zama."
- Muyiwa Adejobi.
Gwamnatin Kebbi Ta Kubutar da Mutane 30 Daga Hannun 'Yan Bindiga
A wani labarin kuma Gwamnatin jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta ceto mutum 30 da suka fito daga jihohi 3 daga hannun 'yan bindiga.
Shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasagu, Honorabul Hussaini Aliyu Bena, shi ne ya bayyana haka ga 'yan jarida a Birnin Kebbi ranar Laraba.
Asali: Legit.ng