Dan Takarar Gwamnan SDP a Jihar Kogi Ya Bankado Shirin Ganin Bayansa
- Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Muritala Yakubu Ajaka ya yi zargin akwai masu son ganin bayansa
- Muritala Ajaka ya ce haskawar da tauraruwarsa ke yi a jihar ne ya sanya ake ƙoƙarin ganin ya bar duniya
- Ɗan takarar dai basa ga maciji da gwamnan jihar Yahaya Bello, tun bayan da ya tsallaka zuwa jam'iyyar SDP daga APC
Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Alhaji Muritala Yakubu Ajaka, ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin ganin bayansa saboda ƙarin farin jinin da yake samu a jihar.
Ajaka ya shiga takun saƙa ne da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC, Usman Ododo, bayan ya fice daga jam'iyyar APC lokacin da aka gudanar da zaɓen fidda gwanin gwamna na jam'iyyar.
Jaridar Nigerian Tribune ta ambato Ajaka a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels Tv na cewa farin jininsa ne ya sanya gwamnatin jihar ke takun saƙa da shi.
Ɗan takarar na jam'iyyar APC ya bayyana cewa da bai shiga takarar neman gwamnan jihar ba idan da jam'iyyar APC da Yahaya Bello sun kai tikitin takarar gwamnan yankin Kogi ta Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa yakamata ace jam'iyyar APC ta kai tikitin takarar gwamnan yankin Kogi ta Yamma saboda lokacin mutanen Okun ne na samar da gwamnan jihar.
"Maganar gaskiya idan da Yahaya Bello ya yi wa al'ummar jihar Kogi adalci. Da ya ɗauko wani daga yankin Kogi ta Yamma, tabbas da mun gayawa mutanenmu su jira. Da mun bi abinda gwamnan ya ce." A cewarsa.
Matakin da ya ɗauka kan barazanar da ake yi wa rayuwarsa
Muritala Ajaka ya bayyana cewa tuni ya fara ɗaukar matakai kan barazanar da ake yi wa rayuwarsa, cewar rahoton Channels tv.
A cewarsa ya rubuta wasiƙa zuwa ga babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da babban Sufeta Janar na ƴan sanda, cewa duk abinda ya same shi, iyalansa ko ƴan tawagar yaƙin neman zaɓensa, lallai alhakin yana kan gwamnatin jihar.
Bata-Gari Sun Lalata Sakatariyar Jam'iyyae SDP
A wani labarin na daban kuma, wasu ɓata-gari sun kai farmaki kan sakatariyar jam'iyyar SDP a jihar Kogi.
Ɓata-garin waɗanda ake zargin turo su aka yi sun dai lalata muhimman kayayyaki tare da ƙona wasu a sakatariyar jam'iyyar.
Asali: Legit.ng