Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele A Cikin Mako 1, Ta Bayyana Dalillai

Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele A Cikin Mako 1, Ta Bayyana Dalillai

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar DSS ta sake dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Kotun ta ce hukumar ta gaggauta sakin nasa cikin mako daya ko ta mika shi kotu idan ta da wani korafi
  • Alkalin kotun, Hamzu Muazu ya ce tsare Emefiele ba tare da ka'ida ba tauye masa hakki ne na dan Adam

FCT, Abuja - Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin sake dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a cikin mako daya.

Kotun ta ba da umarnin ne ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS inda ta ce idan ta na da korafi a kan Emefiele ta kai shi kotu.

Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele A Cikin Mako 1 Ko Ta Mika Shi Kotu
Hukuumar DSS Na Zargin Emefiele Da Badakalar Makudan Kudade. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Hamza Muazu ya yi umarnin a ba da belin Emefiele a cikin mako daya idan ba za a tura shi kotu ba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

NLC Za Ta Sa Ƙafar Wando Ɗaya da Bola Tinubu, An Buƙaci Karin 300% a Albashi

DSS na zargin Emefiele da badakalar makudan kudade

Idan ba a manta ba, a ranar 9 ga watan Yuni, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emifiele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan dakatarwar, Tinubu ya bukaci Emifiele ya gaggauta mika duk wasu abubuwa da ke karkashinsa zuwa ga mataikin gwamnan bankin a bangaren ayyuka, Folashodun Adebisi, cewar Tribune.

Kwana daya rak da dakatar da Emiefele, Hukumar Tsaro Farin Kaya (DSS) ta kama Godwin Emiefele bisa zargin wasu badakala.

Ta bakin lauyansa, Joseph Daudu, Emiefele ya shigar da hukumar DSS da ministan shari'a kotu kan tauye masa hakkokinsa da dan kasa.

Yayin hukuncin, kotun ta bayyana cewa tsare Emefiele a ofishin hukumar ba tare da shari'a ba take masa hakkinsa ne, Vanguard ta tattaro.

Ta umarci hukumar ta sake Emefiele ko ta mika shi kotu

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Kasa Tinubu Na Ganawa Mai Muhimmanci Da Zulum a Fadar Shugaban Kasa

Ya ce:

"Rike mutum ba bisa ka'ida ba ko mai kankartar shi tauye hakkin dan Adam ne."

Kotun ta kara da cewa tun da zargin da ake wa Emefiele akwai tsarin ba da beli, hukumar ta yi gaggawar ba da belinsa kafin yanke hukunci.

Ya bayyana hukumar a matsayin wata cibiya da ke da alhakin tsaron kasa, ya kamata ta yi aiki bisa tsarin dokar kasa.

Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Karar Emefiele A Watan Yuli

A wani labarin, kotu za ta yanke hukunci a kan karar dakataccen gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.

Rahotanni sun ce kotun ta shirya yanke hukuncin kan tsare Emefiele da hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ta yi ranar 13 ga watan Yuni, 2023.

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN tare da ba da umarnin bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.