An Dakatar Da Kamfanin Jirage Na Max Air Daga Gudanar Da Ayyukan Sufuri a Cikin Najeriya

An Dakatar Da Kamfanin Jirage Na Max Air Daga Gudanar Da Ayyukan Sufuri a Cikin Najeriya

  • Hukumar sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta sanar da dakatar da kamfanin Max Air daga harkokin sufurin cikin gida
  • Sanarwar dai na kunshe ne a cikin wata takarda da aka aikawa kamfanin wacce manema labarai suka samu ranar Alhamis
  • Sanarwar ta bayyana cewa za a baiwa kamfanin izinin ci gaba da harkokinsa in ya cika sharuddan da aka gindaya masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Rahotanni na nuni da cewa an dakatar da ayyukan cikin gida na kamfanin Max Air, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a Najeriya.

Hukumar sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ce ta ba da sanarwar dakatarwar a wata wasiƙa da ta rabawa manema labarai ranar Alhamis.

Sanarwar a cikin wasikar mai lamba NCAA/DG/AIR/11/16/363, NCAA, ta ba da umarnin dakatar da sassan A3 da D43 nau'in jirgin saman Boeing 737 na kamfanin Max Air nan take kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata: Majalisa Za Tayi Binciken Yadda Aka Saida Kadarorin Gwamnati

An dakatar da kamfanin Max Air daga harkokin sufurin cikin gida
An dakatar da kamfanin jiragen sama na Max Air daga harkokin sufurin cikin gida. Hoto: Max Air LTD
Asali: Facebook

Max Air ba zai ci gaba da ayyukan cikin gida ba

Wannan mataki dai na nufin kamfanin na Max Air ba zai ci gaba da gudanar da harkokin sufurin jirage na cikin gida ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar a cikin sakon da aika aikawa kamfanin, ta bukaci kamfanin ya dakatar da duk wasu ayyuka da jiragensa kirar Boeing B737 ba tare da bata lokaci ba.

Matakin na zuwa ne a lokacin da aka samu korafe-korafe kan jiragen na Max Air kirar Boeing B737 kamar yadda sanarwar da daraktan aikace-aikace na hukumar sufurin saman, Kyaftin Ibrahim Bello Dambazau ya sanyawa hannu.

Dalilan da suka sa aka dakatar da jiragen na Max Air

Daga cikin manyan dalilan da suka janyowa kamfanin na Max Air dakatarwa, akwai matsalar da aka samu da jirgin na Max Air a kwanakin baya, inda tayoyin daya daga cikin jiragen, wanda ya taso daga Yola suka kama da wuta.

Kara karanta wannan

Za a rina: Gwamna ya umarci farfesan halayyar dan Adam ya zauna da dalibar da ta kara sakamakon JAMB

Tun bayan tasowar jirgin a ranar 7 ga watan Mayu, daga Yola babban birnin jihar Adamawa, tayoyinsa suka fara ci da wuta inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

An kara samun wani tsaiko da jirgin na Max Air kirar B737-300 gabanin ya tashi daga filin jirgin sama na Yola a ranar 7 ga watan Yulin 2023.

Haka nan ma, jirgin na Max Air kirar B737-400 ya samu wani tsaiko na daukar zafi da ya sa jirgin fasa tashi, a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2023.

A ranar 11 ga watan Yulin 2023, an samu wata matsala da ke da alaka da daukar zafi a wani jirgi na Max Air da ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Daga karshe, sanarwar ta ce ba za a ba kamfanin izinin ci gaba da gudanar da harkokinsa na sufurin cikin gida ba har sai ya gyara duka matsalolin.

Kara karanta wannan

Ta Bayyana: Tambuwal, Yari, Wammako Da Wasu Tsaffin Gwamoni 11 Da Ke Karbar Fanso Bayan Zama Sanatoci

Fasinja ya bude kofar jirgin sama ana cikin shilla gudu

Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku rahoto kan wani fasinjan jirgin sama da ya bude kofa ana cikin sheka gudu.

Fasinjan ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda ji da yi numfashinsa na neman daukewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng