Mata Da Miji Sun Yi Basaja a Matsayin Sabbin Shiga Musulunci Inda Suka Yi Wa Babban Liman Sata a Yobe
- Wani miji da matarsa sun faɗa komar 'yan sandan jihar Yobe bayan tafkawa wani limami sata
- Ma'auratan sun yi basajar cewa suna so su karɓi Musulunci ne, inda daga bisa ni suka aikata ta'asar
- Sun yi awon gaba da babur ɗin ɗaya daga cikin 'ya'yan limamin da suka sauka a wurinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yobe - Jami’an ‘yan sandan jihar Yobe sun cafke wasu ma’aurata, Abdullahi Ibrahim da Khadija Ali bisa zargin satar babur na wani malamin addinin musulunci a ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu kamar yadda PM News ta wallafa.
Sun je wajen liman da zummar suna so su karɓi Musulunci
Kakakin ya ce Ibrahim mai shekaru 21 da Khadija mai shekaru 20, a ranar 4 ga watan Yuni sun je, wajen malamin da zummar cewa suna so su Musulunta.
Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa sun gabatar da kansu a matsayin Jude Emmanuel, ɗan ƙabilar Birom daga Farar-Kasa a Barkin Ladin jihar Filato da matarsa, da ta bayyana sunanta da Peace Sunday.
Kakakin ya bayyana cewa bayan musuluntar da su ne, sai aka ce su zauna wajen babban Limamin Fika domin koyar da su ilimin addini da sauran abubuwa.
Abdullahi ya ɗauke babur a gidan limamin da suke zaune wurinsa
Dungus ya kuma ƙara da cewa bayan kwana ɗaya ne Abdullahi ya sanar da limamin cewa yana so ya samu toka daga wurin da tsawa ta faɗa don ya haɗa wani magani.
A kalamansa ya ci gaba da cewa:
“Liman ɗin ya haɗa shi da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa don ya kai shi wani daji da ke kusa. Bayan isarsu wurin ne wanda ake zargin ya ɗebo ƙasar ya taho da ita.”
“A rana ta uku mutumin ya ƙara neman a sake kai shi wurin da zummar ɗebowa matarsa ƙasar. A rannan sai limamin ya sa ɗansa ya kai shi a kan babur ɗinsa.”
“Isarsu wurin ke da wuya sai suka yi wa yaron fashin babur ɗin sannan kuma suka arce da shi.”
Dungus ya bayyana cewa a ranar 1 ga watan Yuli, 'yan sanda sun samu bayanai da ke nuni da cewa an ga ma’auratan a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno, suna shirin aikata makamancin abinda suka aikata.
Sai dai ya ce dubunsu ta cika a ranar 5 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 02:00 na rana, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar cafke su.
Daily Post ta ruwaito cewa Abdullahi asalinsa Musulmi ne, kuma sunansa kenan Abdullahi, ɗan garin Sabon Garin Mai Mala da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Haka nan ita ma matar ainihin sunanta kenan Khadija Ali, yar asalin jihar Gombe.
Ya taɓa aikata irin wannan aika-aikar a jihar Gombe
Haruna Muhammad, ladanin masallacin juma'a a Sangaru da ke ƙaramar hukumar Funakayen jihar Gombe, a zantawarsa da Legit.ng, ya bayyana yadda wannan mutumin ya yi zamba cikin aminci a garinsu.
Ya ce ya zo musu ne da suna Bala, kuma da sigar cewa ya samu saɓani da iyayensa waɗanda Kiristoci ne sakamakon musulunta da ya yi.
Hakan ta sa aka tausaya masa, inda Yariman garin, Alhaji Adamu Yariman Sangaru ya ba shi masauki a wurinsa.
Haruna ya ƙara da cewa mutumin ya zauna a tare da Yariman inda har ya zamto an saba da shi, ana hulɗoɗi na yau da kullum a tare da shi.
Ya bayyana cewa ya yaudari Yariman, inda ya karɓi babur ɗinsa da zummar zai je kasuwa sayo littattafan koyon addini.
A cewar Haruna:
“Kullum da safe zaka sameshi yana riƙe da allo yana karatu ko nima ranar da naje zan gaisa da Yarima, nasameshi yana karatu a kofar gida.”
“Kai ƙarshe in gayama, saida yadawo direban yarima kullum Jumma'a shi yake tuƙoshi a mota ya kawoshi masallaci.”
“Kafin yasamu damar fecewa da mashin motar yariman yayi hari Allah ya kiyaye.”
“Saudayawa sai yasamu ɗan yariman wanda ake kira da Ahmadi sai yace yadauko musu mota suje yawo shi kuwa yaron sai yaki, haka akayi ta bugawa na tsawon kwanakai baiyi nasaraba.”
“Ya karɓi mashin ɗin Yariman da misalin karfe 04:00 na yamma, inda ya goya ɗan yariman da jikansa ɗaya da nufin zasu je kasuwa don ya sayo ƙawa'idi.”
“Suna zuwa kasuwa sai yaje ya sayi ƙawa'idi yaje wajen wani tela yace yaran su jirashi a nan zai sayo wani abu, a taƙaice dai wannan itace tafiyar da bai dawoba har yau ɗin nan.”
Tsawa ta kashe masu garkuwa da mutane 3 a jihar kwara
Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a baya kan wasu masu garkuwa da mutane su uku, da suka gamu da ajalinsu a yayin da tsawa ta faɗa musu.
Wannan lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Yuli, a ƙauyen Oro Ago, ƙaramar hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara.
Asali: Legit.ng