Shugaba Tinubu Ya Gana da Sabon Mukaddashin Shugaban EFCC a Villa

Shugaba Tinubu Ya Gana da Sabon Mukaddashin Shugaban EFCC a Villa

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da masu almundahana ta ƙasa (EFCC)
  • Wannan ne karon farko da Tinubu ya karbi bakuncin Abdulkarim Chukkol a Villa tun bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa
  • A ranar 14 ga watan Yuni, shugaban kasa ya dakatar da Bawa kuma ya umarci ya miƙa wa Mista Chikkol ragamar EFCC nan take

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da sabon muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).

Tinubu ya gana da sabon muƙaddashin shugaban EFCC, Abdulkarim Chukkol, a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.

Shugaban kasa Tinubu tare da shugaban EFCC, Abdulkarim Chukkol.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Sabon Mukaddashin Shugaban EFCC a Villa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkoki kafafen sada zumunta na zamani, D. Olusegun ne ya tabbatar da haka a shafinsa na tuwita.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Ya rubuta a shafinsa cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin muƙaddashin shugaban hukumar EFCC, Mista Abdulkarim Chukkol a fadarsa."

Wannan ganawa ta ranar Laraba na zuwa ne makonni hudu bayan Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban EFCC har sai baba ta gani daga ranar 14 ga watan Yuni, 2023.

Meyasa shugaba Tinubu ya dakatar da Bawa?

Shugaban ƙasa ya dakatar da Bawa ne domin, "Ba da cikakkiyar damar bincikar ayyukan da ya yi lokacin yana ofis."

Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey, ya ce dakatarwan ta biyo bayan yawaitar tuhume-tuhume kan Bawa, wanda ake zargin ya ci mutuncin ofishinsa.

Nan take shugaban ƙasa ya umarci Bawa ya gaggauta mika ragamar tafiyar da ofishinsa hannun daraktan sashin ayyuka na hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

Jim kaɗan bayan haka, hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS) ta yi ram da Mista Bawa kuma ta titsiye shi da tambayoyi a ofishinta, har yanzu yana can a tsare.

Shugaba Tinubu Zai Nada Ministoci 36 Zuwa 42 a Gwamnatinsa

A wani rahoton na daban kuma Sakataren APC ya bayyana yawan Ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai naɗa a sabuwar gwamnatinsa.

Sanata Iyiola Omisore, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , zai naɗa ministoci 36 zuwa 42 a gwamnati nan da makonni biyu masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262