Rikita-rikita Yayin Da Mai Kara Ya Fashe Da Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Ke Kara Alfarma, Ya Fadi Dalilansa

Rikita-rikita Yayin Da Mai Kara Ya Fashe Da Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Ke Kara Alfarma, Ya Fadi Dalilansa

  • An shiga wani yanayi a kotu bayan mai kara ya fashe da kuka kan hukuncin da kotu ta yanke wa wanda yake kara
  • James Bassey ya kai karar Pius Savoir bisa zargin sata masa dutsen guga a Badagry da ke jihar Lagos
  • Bayan alkali ya yanke hukunci, sai Bassey ya durkusa ya na rokon yi wa Pius alfarma saboda irin taimakonsa da yake

Jihar Lagos - Yayin zaman kotun majistare da ke Badagry a jihar Lagos, mutane sun sha mamaki yayin da mai kara ke nema wa wanda ake kara alfarma.

Yayin zaman kotun a yau Laraba 12 ga watan Yuli, mai karar James Bassey ya durkusa har kasa ya na kuka don nema wa wanda ake zargi hukunci mai sauki.

Rikici Yayin Da Mai Kara Ya Fashe Da Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Ke Kara Alfarma A Kotu
Mai Kara Ya Durkusa Yana Kuka Ya Na Nema Wa Wanda Ya Kai Kara Kotu Alfarma. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ana zargin Pius Savoir ne mai sana'ar wanki da guga da satar dutsen guga da kudinsa ya kai N20,000.

Kara karanta wannan

Muje Zuwa: El-Rufai Ya Magantu Kan Yadda Kamun Ludayin Gwamnatin Shugaba Tinubu Ya Kawo Sauyi

Mai karar ya durkusa ya na neman alfarma wa wanda ya ke karar

Bayan yanke masa daurin wata daya a gidan kaso, sai James wanda ya kawo karar ya durkusa ya na nema masa afuwa, cewar Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya ya daure Savoir wata daya a gidan kaso bayan amsa laifukan da ake tuhumarsa da bayyana shaidu.

Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun ya yi alkawarin yin sassauci tun da wannan shi ne karon farko na aikata laifin, Daily Nigerian ta tattaro.

Daga bisani ya tasa keyar Savoir gidan kaso na mako daya, yayin da zai karasa sauran makwanni uku ya na kai ziyara ofishin 'yan sanda don yin aikin lada.

Cikin kuka ya bayyana dalilinsa na nema wa Pius alfarma

Yanke hukuncin ke da wuya, Bassey ya fashe da kuka inda ya roki kotun ta yiwa Savoir alfarma.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Motar da ta dauko masu zuwa 'party' ta yi karo da motar yashi, mutum 20 sun mutu

Bassey ya ce:

"Ya mai shari'a, ba ni da mata ko 'ya'ya wannan mutumin shi ya ke kula da ni.
"Shi ya ke taimakamin da ayyuka a gida da kuma yi min tausa, kawai naga satar ta yi yawa ne shiyasa na kawo kararsa.
"Idan ka tura shi gidan kaso, babu mai taimako na hakan zai sa na rasa raina."

Kotu Ta Tsare Wani Matashi Kan Zargin Satar Jaririya ’Yar Watanni 2

A wani labarin, kotu ta tsare wani matashi bisa zargin satar jaririya 'yar kimanin watanni biyu.

Wanda ake zargin Solomon Kingsley ya saci yarinyar ne da ya yi ikirarin 'yarsa ce kafin daga bisani ya sauya magana.

Tun farko Solomon ya fada wa 'yan sanda cewa sun taba yin mu'amala a otal da Joy wacce ita ce mahaifiyar jaririyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.