Gwamnan Benue Ya Bayyana Hakikanin Masu Aikata Kashe-Kashe a Jihar

Gwamnan Benue Ya Bayyana Hakikanin Masu Aikata Kashe-Kashe a Jihar

  • Gwamnan jihar Benue ya bayyana cewa ƴan cikin gida ne ke aikata kashe-kashen da ake fama da su a jihar
  • Gwamna Hyacinth Alia ya ce ba za su zura ido suna kallon marasa son ganin zaman lafiya ba a jihar na cin karensu babu babbaka
  • Gwamnan ya yi muhimmin gargaɗin cewa duk waɗanda ba za su bi doka da oda ba a jihar to su tattara kayansu su ƙara gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Benue - Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya nuna damuwarsa kan kashe-kashen da ke aukuwa a ƙaramar hukumar Ukum ta jihar.

Rabaran Hyacinth Alia ya bayyana cewa masu aikata kashe-kashen ƴan cikin gida ne ba baƙi ba, cewar rahoton Vanguard.

Gwamnan Benue ya bayyana masu aikata kashe-kashe a jihar
Gwamna Alia ya ce yan cikin gida ke aikatawa ba baki ba Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A ranar Asabar da ta gabata ne dai wasu gungun ƴan bindiga suka farmaki ƙauyen Akpuuna cikin ƙaramar hukumar Ukum, inda suka halaka sama da mutum 30 da raunata wasu da dama sannan suka ƙona gidaje da kasuwar ƙauyen.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Gwamna Alia ya ziyarci ƙauyen

Gwamna Alia, wanda ya ziyarci ƙauyen a ranar Talata, ya nuna kaɗuwarsa kan kashe-kashen da ɓarnar da aka yi a yankin inda ya ce sam hakan ba abinda za a zura ido ba ne a ƙyale.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya nuna baƙin cikinsa kan kashe-kashen inda ya ce ba abinda al'ummar jihar Benue ke fatan samu ba kenan, jaridar The Punch ta yi rahoto.

A kalamansa:

"Akwai mabambantan labarai kan haƙiƙanin abinda ya faru. Ina tunanin waɗanda suka bada labarinsu a nan, idan aka ƙebe da su za su bayyana haƙiƙanin abinda ya faru."
"Suna sane da waɗanda su ke da hannu a wannan mummunan harin. Za mu tattauna da su domin zaƙulo haƙiƙanin abinda ya haddasa hakan. Amma sam ba za mu ci gaba da yarda da hakan ba. Jihar Benue jiha ce mai zaman lafiya sannan dole zaman lafiya ya dawo a Benue."

Kara karanta wannan

Hare-Haren 'Yan Bindiga: Dan Majalisar Tarayya Ya Buƙaci Mutanen Jiharsa Su Kare Kansu

"Waɗannan kashe-kashen ƴan cikin gida ne ke yinsu, babu wanda zai zo daga waje ya yi waɗannan kashe-kashen. Daga cikinku ne, ƴan'uwa na kuna halaka juna, daga cikin gida ne sannan dole a dai na aikata hakan."
"A ce ƙauye ɗaya gaba ɗaya an shafe shi, ta yaya za ayi bayanin hakan? Don haka idan Benue ta yi mu ku kaɗan ku tattara kayanku ku ɓace. Amma idan kuka tsaya a jihar nan dole ku bi doka da oda. Babu wani abu saɓanin hakan."

Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Kashe-Kashen Benue Da Plateau

A wani labarin na daban kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai ɗa munanan kashe-kashen da ake yi a jihohin Plateau da Benue.

Shugaban ƙasar ya umarci jami'an tsaro da su tabbatar cewa sun zaƙulo dukkanin masu hannu a kashe-kashen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng