Kundin Tarihi Na Guinness: An Gargadi 'Yan Najeriya Kan Kawo Shiririta Yayin Kafa Tarihi, Ya Bayyana Matakai
- Tun bayan kafa tarihi da Hilda Baci ta yi na wacce ta fi kowa dadewa ta na girki, 'yan Najeriya suka mai da abin gasa
- Hilda ta yi girki fiye da sa'o'i 100 inda ta doke mai rike da kambun daga India, Lata Tondon da ta yi sa'o'i 87
- Daga nan 'yan Najeriya da sauran kasashe musamman a Nahiyar Afirka suka yi ta kokarin neman kafa tarihi a bangarori daban-daban
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kundin tarihi na Guinness ya gargadi 'yan Najeriya da su guji kokarin kawo shiririta da nufin kafa wata tarihi.
Wannan gargadi na zuwa ne bayan wani ya yi kokarin kafa tarihi na 'Manufa' da 'Numfashi' da kuma wani matashi da ya fara kuka don kafa tarihi, cewar Legit.ng.
Kamfanin ya gargadi 'yan Najeriya akan kafa tarihi barkatai
A sanarwar da TheCable ta tattaro, kamfanin ya wallafa a manhajar 'Threads' kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Don Allah wannan kafa tarihi ya isa haka."
Wannan na zuwa ne bayan wani dan wasan barkwanci daga Kamaru ya fara gasar wanda ya fi kowa dadewa ya na kuka.
'Yan Najeriya da dama sun shiga kokarin kafa tarihi bayan Baci Hilda ta kafa tarihin wacce ta fi kowa dadewa ta na girki.
A cikin sanarwar, kamfanin da ke Burtaniya ya shawarci masu son kafa tarihi da su jira sai sun sami amincewa daga jami'ansu.
Yadda 'yan Najeriya suka ca akan kundin Guinness don kafa tarihi
Bayan Hilda Baci ta kafa nata tarihi, 'yan Najeriya da sauran kasashe musamman a Nahiyar Afirka sun fara kokarin kafa tarihi a bangarori da dama.
Bayan Hilda, wata mai girki, Damilola Adeparusi ta fara girki har na tsawon kwanaki biyar don kafa tarihi.
Yayin da Adeyeye Adeola ta yi yunkurin karya tarihin Hilda don yin girki a sa'o'i 150, GistReel ta tattaro.
Har ila yau, Tomitofe Adebayo da ke Ibadan na jihar Oyo ta yi kokarin yin girki har na tsawon sa'o'i 120.
Danny Zara daga kasar Kamaru ta bayyana aniyarta na kafa tarihin wacce ta fi kowa dadewa ta na saduwa.
Yayin da Joyce Ijeoma ta fara tausa don kafa tarihi kafin ta fadi bayan wasu sa'o'i ta na tausar.
Sannan wani lakcara a jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke jihar Ekiti, Hassan Bature Joshua ya ce zai koyar da dalibai na sa'o'i 150 don kafa tarihi.
Kundin Bajinta Na Guinness Ya Lamuncewa Dan Najeriya Yin Waka Na Sa'o'i 200
A wani labarin, Kamfanin Guinness ya bai wa dan Najeriya damar yin waka na sa'o'i 200 don kafa tarihi.
Matashin mai suna Oluwatobi Kufeji ya fara wakar a jihar Lagos don zama wanda ya fi kowa dadewa yana waka.
A ranar 10 ga watan Yuni, matashin ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa kamfanin ya lamunce masa.
Asali: Legit.ng