'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasto Da Wasu Mutum Uku a Jihar Ebonyi
- Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban fasto da wasu mutum uku a jihar Ebonyi da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya
- Ƴan bindigan sun sace Rev. Fr. Joseph Azubuike ne a kusa da cocinsa bayan ya dawo daga ayyukan coci
- Shugaban coci Katolika ta jihar wanda ya tabbatar da sace faston ya buƙaci ayi addu'o'i domin sako su cikin aminci
Jihar Ebonyi - Ƴan bindiga sun sace wani faston ɗariƙar Katolika, Rev. Fr. Joseph Azubuike da wasu mutum uku a jihar Ebonyi.
Jaridar The Punch ta tattaro cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da su ne a ranar Litinin, 10 ga watan Yulin 2023.
Fr. Azubuike shi ne shugaban cocin St. Charles Parish, a ƙauyen Mgbaleze na yankin Isu a ƙaramar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.
Shugaban babbar cocin Katolika ta Abakaliki, Rev Fr. Mathew Opoke, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata cikin wata sanarwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa an sace Fr. Azubuike ne a kusa da cocinsa bayan ya dawo daga ayyukan coci.
Ƴan bindigan sun nemi a basu kuɗin fansa kafin su sako faston
Opoke ya bayyana cewa ƴan bindigan da su ka yi garkuwa da shi ɗin sun tuntiɓi cocin inda suka buƙaci a basu maƙudan kuɗaɗe a matsayin kuɗin fansa, cewar rahoton Leadership.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Muna roƙon addu'ar sako Rev. Fr. Joseph Azubuike wanda aka sace a jiya Litinin, 10 ga watan Yulin 2023 a kusa da cocinsa bayan ya dawo daga ayyukan coci."
"Waɗanda suka sace su suna neman a basu kuɗin fansa amma da addu'o'inku za a dawo mana da su ba tare da wani sharaɗi ɓa."
Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Onome Onovwakpoyeya, kan sace faston da ragowar mutanen.
'Yan Bindiga Sun Halaka 'Yan Sanda a Zamfara
A wani labarin na daban kuma ƴan bindiga sun halaka jami'an ƴan sanda huɗu har lahira a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan dai sun yi wa jami'an ƴan sandan kwanton ɓauna ne suna tsaka da sintiri a wajen shingen bincikensu akan titi.
Asali: Legit.ng