Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Ya Samu Sabon Mukami
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu sabon mukami bayan barin ofis
- Kimanin wata shida bayan barin Aso Rock, an nada Osinbajo mashawarci na duniya ga Global Energy Alliance for People and Planet
- Farfesan na shari'a, wanda ya ce ya yi murna, ya kara da cewa a shirye ya ke inganta kasan Afirka a kasuwar carbon na duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya samu sabon mukami makonni shida bayan barin Aso Rock, babban birnin tarayya, Abuja.
Farfesa Osinbajo ya sanar da cewa an nada shi a matsayin mai bada shawara na duniya ga kamfanin Global Energy Alliance for People and Planet.
Ya sanar da hakan a ranar Talata, 11 ga watan July, ta shafinsa na Twitter @ProfOsinbajo.
"Ina farin cikin sanar da cewa an nada ni mashawarci na duniya ga Global Energy Alliance for People @EnergyAlliance. Tare, za mu yi aiki don kawo jari a bangaren makamashi mai tsafta da inganta kason Afirka a kasuwar carbon ta hanyar #ACMI"
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa alhakin da ya rataya a wuyansa shi ne na bude hanyoyin samar da makamashi mai tsafta da kuma habaka kason Afirka a kasuwar carbon ta duniya.
Yemi Osinbajo Ya Samu Aikin Farko Bayan Barin Aso Rock
A wani rahoton daban, Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya tafi kasar Sierra Leone domin aikin zabe da aka shirya yi a kasar.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta, Farfesa Osinbajo zai jagoranci tawagar kungiyar kasashen da Birtaniya ta raina (Commonwealth (COG), don sa ido a kan zaben da za a yi.
Osinbajo ya ce zai yi aikin sa ido kan zaben ne sati uku bayan saukarsa daga kujerar mataimakin shugaban kasar Najeriya.
Sabbin Shugabannin Kwamitoci 8 Da Mataimakansu Da Aka Zaba A Majalisar Dattawa
A zaman farko da Majalisar Dattawa ta yi a wannan makon an kafa kwamitoci da za su jagoranci sanatoci a majalisar dattawa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sanar da shugabannin kwamitoci na musamman da mataimakansu a majalisar.
Sanatoci daga jam'iyyun APC, PDP da SDP duk sun samu makamai daban-daban.
Asali: Legit.ng