Budurwa Ta Gayyaci Samarinta 3 Don Su Tayata Kwashe Kaya Zuwa Sabon Gida Ba Tare Da Sun Sani Ba

Budurwa Ta Gayyaci Samarinta 3 Don Su Tayata Kwashe Kaya Zuwa Sabon Gida Ba Tare Da Sun Sani Ba

  • Wata matashiya ta rubuta a twitter cewa ta yi wasa da hankalin samarinta wajen tayata kwashe kaya zuwa sabon gida ta hanyar yi masu karyan cewa yan uwanta ne
  • Rubutun ya yadu kuma ya samu martani daban-daban daga sauran masu amfani da twitter
  • Matashiyar bata yi bayanin yadda ta dunga soyayya da su ukun ba ko kuma sun gano cewa karya take yi masu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rubutun da wata matashiya ta yi a twitter na yadda ta yi wa samarinta uku dabara har suka tayata kwashe kayanta zuwa sabon gida ya yadu a soshiyal midiya.

A rubutun wanda @muvatone ta yi a ranar 9 ga watan Yulin 2023,bta yi ikirarin cewa ta fada ma kowanne daga cikin masoyan nata cewa sauran yan uwanta ne daga bangaren mahaifinta.

Hoto gida da wasu mutane
Budurwa Ta Gayyaci Samarinta 3 Don Su Tayata Kwashe Kaya Zuwa Sabon Gida Ba Tare Da Sun Sani Ba Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Budurwa ta yi wasa da hankalin samarinta uku

Kara karanta wannan

Wa Zai Auro Wani? Rikita-rikita Bayan Amarya Ta Ce Dole Sai Dai Miji Ya Koma Amfani Da Sunanta

Ta kara da cewar suna ta gaishe da junansu da yin yar hira kadan-kadan a tsakaninsu, ba tare da sun san gaskiyar lamari ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rubutun na twitter wanda ya samu dubban 'likes' ya haddasa cece-kuce sosai daga masu amfani da dandalin.

Wasu sun jinjina mata kan kasancewarta mai hikima, yayin da wasu suka soke ta kan rashin gaskiya da cin amana.

Wasu sun kuma tambaya ko da gaske ne rubutun inda suka yi tunanin ko wasa ne ko zolaya.

Matashiyar bata bayyana ko wani daga cikin samarin nata ya gano gaskiya ba ko yadda ta dunga fama da soyayya da mutanen uku a lokaci guda ba tare da sun sani ba.

Ga wallafar tata a kasa:

Martanin jama'a

@tiagetssocial ta ce:

"Da babban jin dadin shine ace ki sa dukkansu sun 3 su biya wadanda za su kwashe maki kaya."

Kara karanta wannan

“Dukana Take Yi”: Miji Ya Maka Matarsa a Kotu, Ya Fadi Wahalar Da Yake Sha a Hannunta

@thundacatatl ta yi martani:

"Aminiyata ta yi irin wannan ."

@nathan_oji:

"Idan har dukkansu suna samun biyan bukata."

@Ts_Dollhouse:

"Akwai dadi har sai daya daga cikinsu ya kama ta."

Budurwa ta shiga tasku bayan saurayin da ta yi wa alkawarin aure ya hana ta zuwa wajen daurin aurenta

A wani labari na daban, wata budurwa ta shiga tsaka mai wuya bayan saurayin da ta yi wa alkawarin aure ya hana ta zuwa wajen daurin aurenta.

Matashiyar wacce ta yi wa maza biyu alkawarin aure ta shirya da angonta za su wajen da za a daura masu aure lokacin da saurayin ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng