Gwamna Mai Mala Buni Yana Abuja Nemo Masu Zuba Hannun Jari a Jihar Yobe, Tsohon Hadiminsa
- Bayanan inda gwamnan jihar Yobe ya shiga bayan sake ɗarewa kan kujerar mulkin jihar a karo na biyu sun fito
- Tsohon hadimin gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa gwamnan yana binrin tarayya Abuja nemo masu zuba hannun jari a jihar
- Hakan na zuwa ne dai bayan mutanen jihar sun yi ta caccakar gwamnan kan rashin zaman da yake yi a jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Yobe - Tsohon hadimin gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, Abdulmumin Liman, ya bayyana cewa rashin zaman gwamnan a jihar ya faru ne domin zuwa neman masu zuba hannun jari a jihar.
Buni, wanda aka sake zaɓa karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Yobe, ya kwashe kwanaki babu ɗuriyarsa a jihar, cewar rahoton The Punch.

Source: UGC
Mutane suna ta caccakar gwamnan

Kara karanta wannan
An Shiga Rudani Yayin da Jami'an Amotekun Suka Halaka Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo
Lamarin dai ya sanya mutanen jihar na ta gunaguni kan inda gwamnan ya shiga. Wasu daga cikinsu sun garzaya Soshiyal midiya domin caccakar rashin zaman gwamnan a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ɗaya daga cikinsu mai suna Abdulazeez Hassan, ya koka a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta:
"Kwana 33 har yanzu muna ci gaba da ƙirgawa...komai ya yi daidai a nan jihar Yobe."
Wani mai amfani da da sunan @alhassan_bagare, a Twitter ya rubuta:
"Don Allah ku gaya masa ya dawo jihar da yake mulki ba wai ya maƙale a can ba."
Dalilin gwamnan na komawa birnin tarayya Abuja
Da yake magana kan lamarin, tsohon hadimin gwamnan, ya bayyana cewa gwamnan yana birnin tarayya Abuja inda yake taruka da masu zuba hannun jari na ƙasashen waje kan hanyoyin da za a ƙara samar da kuɗaɗen shiga ga jihar.
A kalamansa:
"Gwamnan yana can yana ta tattaunawa. Yana tattaunawa da jakadu da masu zuba hannun jari na ƙasashen waje domin ciyar da jihar gaba. Ba mu tsammanin ya zauna a jihar Yobe, Abuja nan ne zai haɗu da manyan mutane da ƴan kasuwa domin samo wani abu ga jihar. Don haka ba wai zaune kawai yake ba a can."
"Ba zai yiwu kawai ya zauna a Damaturu ba, dole ya fita ya samo abubuwan ci gaba da za su bunƙasa jihar. Jihar Yobe ba ta samar da kuɗin shiga mai yawa. A matsayin shugaba dole ya fita ya nemo ci gaba."
"Mutane kawai suna son ganin shi ne a Damaturu amma a Abujan da yake ba wai barci kawai yake ya tashi ba. Wasu lokutan a matsayin shugaba dole ya fita waje ya samo abubuwan ci gaba ga jihar.
Mai Mala Buni Ya Yaba Da Nade-Naden Shugaba Tinubu
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya yaba da naɗin sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Tinubu ya yi a ƙasar nan.
Gwamna Mai Mala ya bayyana cewa naɗin hafsoshin tsaron ya nuna cewa matsalar tsaro na dab da yin bankwana a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng
