Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 30 Da 'Yan Ta'adda Suka Sace a Jihar Kebbi
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutum 30 da ƴan ta'adda suka sace a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya
- Mutanen da aka sacen sun shaƙi iskar ƴanci ne bayan dakarun sojojin sun ƙara matsa ƙaimi domin kakkaɓe ƴan ta'adda
- An yaba wa gwamnatin jihar da jami'an tsaro bisa ƙoƙarin da su ke wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kebbi - Dakarun sojoji sun ceto aƙalla mutum 30 da ƴan ta'adda suka sace a ƙaramar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi.
Jaridar The Punch tace shugaban ƙaramar hukumar, Hussaini Bena, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.
Ya yi bayanin cewa yayin da mutum 24 daga cikinsu an sako su ne a ranar Juma'a, ragowar mutum shida sun samu ƴanci ne a ranar Asabar.
Bata-Gari Sun Kai Farmaki Kan Sakatariyar Jam'iyyar SDP a Jihar Kogi, Sun Barnata Dukiya Mai Tarin Yawa
Bena ya yi nuni da cewa biyan bashin kuɗaɗen alawus da jami'an tsaro su ke bi wanda gwamna Nasir Idris ya yi, ya ƙara wa dakarun zumma wacce ta kai ga samun wannan gagarumar nasarar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yaba wa gwamnatin jihar da jami'an tsaro bisa namijin ƙoƙarin da su ke yi
Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa abinda ya kira da gagarumin goyon bayan da ta ke ba jami'an tsaro domin dawo da zaman lafiya a jihar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
"Ina ƙara yaba wa da ƙoƙarin Birgediya Kwamanda mai kula da jihar Kebbi bisa jajricewa da ƙoƙarin dakarunsa, wanda hakan ya sanya aka ceto mutum 30 a cikin kwana biyu kacal." A cewarsa.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutaneɓ da aka sace sun fito ne daga Kotangora a jihar Niger, Danmari, Kaba da Kajiji a jihohin Sokoto da Zamfara, yayin da sauran suka fito daga Bena a jihar Kebbi.
Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu a Jihar Kebbi
A wani labarin na daban kuma, hukumar hana fasa ƙwauri wato Kwastam ta yi kamun kayayyaki masu yawa a jihar Kebbi.
Hukumar ta kama wasu masu kokarin tsallaka Najeriya da buhunan fatu da kuma naman jakuna har 414.
Asali: Legit.ng