An Shiga Jimami a Legas Yayin da Mota Masu Zuwa Taron Liyafa Ta Yi Karo da Tifar Daukar Yashi

An Shiga Jimami a Legas Yayin da Mota Masu Zuwa Taron Liyafa Ta Yi Karo da Tifar Daukar Yashi

  • Allah ya yiwa wasu mutane 20 rasuwa a lokacin da suke kan hanyar zuwa Benin daga jihar Legas a Najeriya
  • An ruwaito cewa, mota bas ce ta yi karo da wata motar daukar yashi, lamarin da ya jawo asarar rayuka
  • Ya zuwa yanzu, an ce duk gawarwakin an kaisu asibitin wani yanki a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya

Jihar Legas - Yau Lahadi ranar bakin ciki ce a unguwar Badagry da ke jihar Legas yayin da wata mota bas mai kujeru 18 cike da ’yan halartar wani taron liyafa ta yi hatsari, inda duk fasinjojin da ke cikinta suka mutu.

Direban bas din da yaronsa ma sun mutu a hatsarin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

An tattaro cewa fasinjojin da suka mutu sun yi hayar motar bas dun ne daga unguwar Yaba da ke Legas domin halartar wani liyafa a jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

Yadda hadari ya kashe mutane a Legas
Jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A daidai ina hadarin ya auku?

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safe a Age-Mowo kusa da Mowo kan hanyar Legas zuwa Badagry, in ji kakakin hukumar kula da ababen hawa ta jihar, Taofiq Adebayo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami'in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Legas (LASTMA) ya shaidawa gidan talabijin din cewa hadarin "ya hada da wata motar bas ta kasuwanci kirar Mazda mai dauke da fasinjoji da wata babbar mota makil cike da yashi."

“Direban motar kasuwan ya rasa yadda zai yi ne a lokacin da ya ga wata babbar mota a gabansa a lokacin da yake kokarin wuce motar ta yashi.
"Nan da nan, mutane 20 suka mutu ciki har da fasinjoji 18 tare da direban bas din kasuwan da yaronsa."

Yadda aka yi da gawarwakin

Adebayo ya ce an kai gawarwakin wadanda abin ya shafa zuwa dakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry, rahoton Ripples Nigeria.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An ga Tsohon Shugaban Kungiyar ASUU Da Ya Bata

Hukumar kula da ababen hawa ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka mutu a hatsarin.

Gangancin tuki da lalacewar hanyoyi na daya daga cikin abubuwan da ke kashe 'yan Najeriya a tituna a lokuta da yawa.

A lokaci irin wannan, aka rasa wani matashi dalibin ajin karshe a jami'ar ABU da ke jihar Kaduna a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.