Najeriya Ta Kara Suna a Duniya, Shugaba Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kungiyar ECOWAS
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar ECOWAS, kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Tinubu ya zama shugaban ECOWAS ne yayin da ya karbi aikin daga hannun Umaro Emba,o, shugaban kasar Guinea Bissau
- Rahoton da muka tattara ya fadi abubuwan ci gaba da shugaban zai samar a matsayinsa na shugaba
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS.
Tinubu ya gaji takwaransa shugaban kasa Umaro Embalo na Guinea Bissau ne a matsayin shugaban na ECOWAS, rahoton gidan talabijin na Channels.

Source: Facebook
A cewarsa bayan kama shugabancin ECOWAS:
"Za mu dauki dimokuradiyya da muhimmanci, dimokuradiyya na da matukar wahala amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka ba Tinubu mukamin
An sanar da fitowar Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS ne a zaman taro na 63 na shugabannin gwamnatocin kasashen ECOWAS, rahoton The Nation.
Taron na gamayyar kasashe karo na 63 shi ne ganawa ta farko da shugaban kasar ya yi a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Wasu abubuwa zai yi?
A matsayinsa na shugaban, zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar kasashe mambobin kungiyar ECOWAS wajen bunkasa tattalin arziki, kwanciyar hankali a siyasance, da hadin gwiwa.
A matsayinsa na sabon shugaban da aka nada, Tinubu zai hada kai tare da kasashe mambobin kungiyar, cibiyoyi da abokan huldar kasa da kasa don aiwatar da tsare-tsaren inganta ci gaban tattalin arziki, hada-hadar kasuwanci a yankin, da ci gaban zamantakewa.
Ana kuma sa ran zai mayar da hankali wajen karfafa hadin gwiwar kungiyar ECOWAS game da barazanar tsaro da samar da hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar wajen tunkarar kalubalen yankin.
Tinubu na wata muhimmiyar ganawa da Shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a a yanzu haka yana ganawa da Shugaban kasar Guinea Bissau kuma Shugaban Shugabannin kasashe a karkashin kungiyar ECOWAS, Umaro Sissoco Embalo a birnin Legas.
Gidan talabijin na Najeriya (NTA) ne ya fitar da labarin ganawar Shugabannin biyu yayin da ya yada wani gajeren bidiyo a shafin Twitter.
Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana manufar wannan ganawar ba, kasancewar bayanai basu fito balo-balo ba game da tattaunawarsu.
Asali: Legit.ng

