Abdulaziz Yari Ya San Dalilin da Ya Sa Muka Gayyace Shi, Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Yiwa ’Yan Jarida Kaca-Kaca
- Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana cewa, rashin iya aiki ne gidajen jaridu suke yada abin da hukumar bata fadi ba
- An ruwaito cewa, DSS ta kama sanata Abdulaziz Yari saboda ya ki amsa wayar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu
- Ya zuwa yanzu, DSS ta ce tana da ikon kama kowa, kuma Yari ya san dalilin da yasa aka kama shi, inji sanarwar da aka fitar
FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta magantu kan gayyatar da ta yiwa sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, Daily Trust ta ruwaito.
An samu rahotanni daban-daban kan zargin kama Yari, amma Peter Afunanya, kakakin rundunar DS, bai amsa tambayoyin da kafafen yada labarai ke ta yi ba.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Afunanya ya karyata rahotannin da suke ta tsokaci kan dalilin da ya sa aka kama Yari, duk da cewa bai bayyana dalilin da ya sa hukumar DSS ta titsye Yarin ba.
An saba aikin jarida wajen bayyana dalilin kama Yari, inji DSS
Afunanya ya kuma bayyana rahotannin da ke cewa an kama sanatan ne saboda ya ki amsa kiran Tinubu a matsayin kololuwar rashin iya aikin jarida, rahoton Daily Sun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika ya karyata rahotannin da ke cewa jami’an DSS sun kai samame ofisoshin hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) da Code of Conduct Bureau (CCB) tare da kwashe wasu takardu daga hukumomin.
Hakazalika, ya ce shi kansa Yarin ya san dalilin da yasa aka kama shi, inda yace hukumar na da ikon kama duk mai laifi don bincikarsa didaida da tanadin doka.
Da yake martani, ya ce:
"Idan za a gayyaci Yari ko wani ko kuma a kai shi gidan yari, Hukumar ba za ta yi jinkirin yin hakan ba matukar hakan bai saba doka ba.”
Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya shaki isakar ‘yanci daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
A daren Asabar 8 ga watan Yuli ne aka saki Sanatan mai wakiltar Zamfara ta Yamma, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Sanata Yari, wanda jami’an DSS suka tsare tare da yi masa tambayoyi a ranar Alhamis, an sake shi ne da misalin karfe 11 na dare.
Asali: Legit.ng