Bayan Wani Dan Lokaci, Tsohon Gwamnan Zamfara Yari Ya Shaki Iskar ’Yanci Daga Hannun Jami’an DSS
- abarin da muke samu ya bayyana cewa, an sako Abdulaziz Yari bayan shafe kwanaki a hannun jami'an DSS
- An ruwaito cewa, an kama Yari ne bayan da aka gayyace shi zuwa hedkwatar hukumar domin yi masa titsiye
- Ya zuwa yanzu, babu wani bayani da ke bayyana dalilin da yasa aka kama tsohon gwamnan na Zamfara
FTC, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya shaki isakar ‘yanci daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
A daren Asabar 8 ga watan Yuli ne aka saki Sanatan mai wakiltar Zamfara ta Yamma, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Sanata Yari, wanda jami’an DSS suka tsare tare da yi masa tambayoyi a ranar Alhamis, an sake shi ne da misalin karfe 11 na dare.
Tun bayan barinsa kujerar gwamna, ana yawan zargin Yari da lamushe wasu kudade da ke da alaka da jihar ta Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dalilin da yasa aka tsare tare da titsiye Yari
Wata kafar yada labarai a baya ta ruwaito cewa DSS ta kama Yari bayan da ya samu kira daga babban daraktan hukumar, Yusuf Bichi, da ya zo hedikwatar DSS domin tattaunawa dashi cikin gaggawa, rahoton gidan talabijin na Arise.
Idan baku manta ba, Yari ya saba tsarin shiyya na APC ta hanyar tsayawa takarar shugaban majalisar dattawa da zabin jam’iyyar, Sanata Godswill Akpabio, wanda a karshe ya yi nasara a zaben shugaban majalisar dattawa.
Yari ya sha fama da rikici da jam’iyyarsa da sauransu. Jam’iyyar tasa ta sha kaye a jiharsa ta Zamfara a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Hukumar DSS ta kama Yari bisa wasu dalilai
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ya na hannun jami’an hukumar DSS masu fararen kaya a Najeriya.
Punch ta ce zuwa yanzu babu wanda ya san dalilin tsare Abdulaziz Yari mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar dattawan kasar nan.
Wata majiya ta ce Yari ya kai kan shi zuwa ofishin hukumar DSS bayan zaman majalisar tarayya da aka yi a ranar Alhamis da ta wuce.
Asali: Legit.ng