Hukumar ICPC Ta Yi Magana Kan Takardun Laifukan Tinubu Da Hadimansa Na Kusa
- Hukumar ICPC ta musanta cewa akwai wasu takardun laifi na Shugaba Bola Tinubu da wasu hadimansa na kusa da shi a hannunta
- Hukumar ta fitar da sanarwa inda ta yi fatali da rahoton cewa hukumar DSS ta ƙwace wasu takardu waɗanda ke ɗauke da laifukan Tinubu da na kusa da shi a wani ofishinta
- Azuka Ogugua, kakakin hukumar ya musanta rahoton inda ya buƙaci al'umma da su yi watsi da shi gaba ɗaya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC) ta bayyana cewa babu wasu takardu masu ɗauke da laifukan Shugaba Tinubu da wasu daga cikin hadimansa na kusa a kowane irin ofishinta a faɗin ƙasar nan.
Hukumar yaƙi da cin hancin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, ta hannun kakakinta Azuka Ogugua, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan
Da Dumi-Dumi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Bayin Allah a Abuja, Rayuka Sun Salwanta

Source: Facebook
Rahoton da ke cewa DSS ta dira a ofishinmu ƙarya ne - ICPC
Legit.ng ta tattaro cewa hukumar ta ICPC tana mayar da martani ne kan wani rahoto da ke cewa hukumar ƴan sandan fararen kaya (DSS) ta dira a wani ofishin hukumar inda ta tafi da wasu takardu da ke ɗauke da laifukan Shugaba Tinubu da hadimansa na kusa da shi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ogugua ya bayyana rahoton a matsayin mara tushe ballantana makama sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi fatali da shi, jaridar The Nation ta yi rahoto.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Don haka hukumar ta musanta rahoton da ke cewa akwai wasu takardun laifukan Shugaba Tinubu ko hadimansa na kusa a hedikwatarta ko ofisoshinta da ke a jihohi. Saboda haka batun cewa an ƙwace waɗannan takardun da babu su ƙarya ce tsagwaronta wacce yakamata al'umma su yi fatali da ita."

Kara karanta wannan
"Ba Haka Aka So Ba": Sabuwar Amarya Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Datse Igiyar Aurenta Da Mijinta, Ta Bayyana Kwakkwaran Dalili 1
Hadimin Atiku Ya Fadi Dalilin Tinubu Na Ba Masu Sukarsa Mukamai
A wani labarin na daban kuma, hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan naɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa Taiwo Oyedele.
Phrank Shuaibu ya bayyana cewa naɗin da Tinubu ya yi wa Taiwo ya yi ne domin ya kulle bakinsa saboda yana ɗaya daga cikin masu sukar kamun ludayin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng