Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bayar Umarnin Rushe Gine-Ginen Da Ke Kan Magudanun Ruwa a Jihar
- Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin rushe gine-ginen da aka yi akan magudanun ruwa a jihar
- Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin kaucewa sake aukuwar ambaliyar ruwa wacce ta auku a jihar
- Gwamnatin tace duk wasu gidaje da gine-ginen da ke kan magudanan ruwa za a rushe su domin samar da hanyar da ruwa zai riƙa wucewa
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin rushe gine-ginen da aka yi su akan magudanun ruwa a ƙoƙarinta na kaucewa sake aukuwar ambaliyar ruwan da aka samu a jihar kwanan nan.
Mataimakin gwamnan jihar, Hon. Faruq Jobe shi ne ya bayar da umarnin ga hukumar tsara birane ta jihar, jim kaɗan bayan ya ziyarci wasu daga cikin wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa, cewar rahoton Vanguard.
Me ya janyo ambaliyar ruwa a jihar?
Jobe ya ɗora alhakin ambaliyar da aka samu a babban birnin jihar kan gine-ginen da aka yi akan magudanun ruwa da zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba a cikin hanyoyin wucewar ruwa, rahoton Thisdaylive ya tabbatar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A dalilin hakan hukumar tsara biranen za ta fara gano gine-ginen da ke akan magudanun ruwa da rushe su domin kaucewa annobar ambaliya a jihar.
A kalamansa:
"Mun bayar da umarni ga hukumar tsara birane da ta rushe dukkanin gidaje da gine-ginen da aka yi su akan magudanun ruwa a yankunan da abin ya shafa domin samar da hanyar da ruwa zai riƙa wucewa."
"Don haka hukumar za ta zauna da waɗanda abin ya shafa domin samar da tsari da samar da hanyar sake gina magudanun ruwan da haramtattun gine-gine suka toshe domin hana aukuwar ambaliyar ruwa a jihar."
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tuni ta fara aikin gyara da faɗaɗa magudanun ruwa a jihar domin magance matsalar ambaliyar ruwa.
Gwamnan Katsina Ya Ba Alhazan Jihar N278m
A wani labarin na daban kuma gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda ya gwangwaje Alhazan jihar da kyautar maƙudan kuɗaɗe a ƙasa mai tsarki.
Gwamnan ya fitar da N278m domin rabawa Alhazan inda ya roƙe su da su yi addu'ar Allah ya kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.
Asali: Legit.ng