Matsalar Tsaro: Gwamna Umar Bago Na Neja Ya Shawarci Mutanen Jihar Su Rage Yawace-Yawace

Matsalar Tsaro: Gwamna Umar Bago Na Neja Ya Shawarci Mutanen Jihar Su Rage Yawace-Yawace

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya shawarci al'ummar jihar da su taƙaita yawan zirga-zirgar da suke yi saboda matsalar tsaro
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai wa sarkin Minna ziyarar jaje dangane da harin da 'yan bindiga suka kai masa
  • Gwamnan ya kuma yi alƙawarin cewa za a bude duka makarantun da aka rufe saboda ayyukan 'yan ta'addan a baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Minna, Jihar Neja - Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya buƙaci al’ummar yankin Kagara da su taƙaita yawan zirga-zirgarsu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai.

Bago ya ba da wannan shawarar ne a lokacin da ya kai ziyarar barka da Sallah ga Sarkin Kagara, Malam Ahmed Garba Gunna (Attahiru ll), a fadarsa da ke Kagara.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran sa, Alhaji Bologi Ibrahim, ya fitar ga manema labarai a Minna ranar Lahadi kamar yadda PM News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB

Gwamnan Neja ya shawarci al'ummar jihar su takaita zirga-zirga
Gwamnan Neja Umar Bago ya nemi 'yan jihar su takit zirga-zirga saboda matsalar tsaro. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Takaita yawace-yawacen jama'a zai taimakawa jami'an tsaro

Bago ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindiga sun yi muni a ɗaukacin masarautar wanda taƙaita zirga-zirgar jama'a, za ta taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙar 'yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa yawaitar tarurruka da yawace-yawace da jama'an karkara ke yi, na shafar ayyukan da jami'an tsaro ke gudanarwa a jihar.

A don haka ne ya ba da shawara cewa a taƙaita yawan taruka da zirga-zirga, inda ya nemi kowa ya yi ƙoƙarin tsayawa cikin yankinsu sai dai in ta kama dole ne su fita.

Gwamna Bago ya kuma yi alƙawarin gina titi mai hannu biyu a Kagara, sannan ya kuma yi alƙawarin sake gina hanyar Minna zuwa Tegina.

Gwamnatin Neja za ta bude makarantun da aka kulle saboda matsalar tsaro

Jaridar Leadership ta kawo wani rahoto, inda gwamnan na jihar Neja ya ba da umarnin a bude makarantun da aka rufe a baya saboda da hare-haren 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Na Yi Wa Jam'iyyar APC Kamfe Amma Ta Bani Kunya, Fittaciyar Jarumar Fina-Finai Na Najeriya

Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, ziyarar jaje kan harin da aka kai fadarsa.

Ya bayyana cewa za a bude makarantun da aka rufe a baya saboda rashin tsaro, sannan kuma ‘yan gudun hiji za su koma gidajensu.

Gwamnan Neja Umar Bago ya rushe hukumar zaɓen jihar (NSIEC)

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto da ke cewa, gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da rushe hukumar zaɓe ta jihar wato NSIEC.

Sanarwar dai ta fito ne ta hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman, wacce ya fitar ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng