Saurayin Wata Amarya Ya Tarwatsa Bikinta, Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

Saurayin Wata Amarya Ya Tarwatsa Bikinta, Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

  • Wata amarya da ta yi wa maza biyu alkawarin aure ta hadu da kalubale na rayuwa yayin da daya daga cikinsu ya gasa mata aya a hannu a ranar aurenta
  • Mutumin, wanda ya ji ciwon abun da budurwar ta yi masa na kin aurensa, ya hana ta zuwa coci a ranar da za a daura mata aure
  • Mutane da dama sun cika da mamakin ko wannan wasan kwaikwayo ne inda wasu suka ce irinta ce macen da bai kamata wani ya aura ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya mai suna @StFrakingKezy ya wallafa bidiyoyi biyu na wani al'amari da ya yi ikirarin ya faru a yankin Apete ta Ibadan a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli.

@StFreakingKezy ya ce amaryar wacce ta yi alkawarin auren maza biyu ta cika da mamaki. Daya daga cikin mazajen da ta yi wa alkawarin aure ya bayyana a ranar daurin aurenta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Janareto Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara

Amarya ta kwanta a kasa yayin da saurayinta ya hargitsa bikinta
Saurayin Wata Amarya Ya Tarwatsa Bikinta, Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo Hoto: @StFrakingKezy
Asali: Twitter

Amarya na birgima a kasa cikin kuka shame-shame

Ya toshe hanya yayin da ita da angon suke hanyar zuwa coci. Bidiyoyin sun nuno tashin hankalin da ake ciki yayin da amaryar ta fadi a kasa tana birgima cike da kosawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano wata mota ta faka a tsakiyar titi. Mutanen da ke daukar bidiyon sun yi martani. Mutane da dama da suka kalli bidiyoyin sun ce watakila wasan kwaikwayo ne ko kuma shiryawa aka yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@iKaptainKush ya ce:

"Amma ai wannan ba suma bane."

@jojorkingsley ya ce:

"Idan wannan ba wasan kwaikwayo bane, an ceto angon daga tashin hankalin shekaru 70, rainon 'ya'yan da ba nasa ba, ka ji tsoron mace."

@self_lost34 ya ce:

"Wannan shine abun da muke magana a kan iyaye da ba nagari ba.....Na tabbata iyayenta suna ta karbar kudade daga wajen mazajen biyu. Na so ina ma ace zan iya rubuta labarin na abokina."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zubawa Ango Abinci Yayin da Take Kokarin Manna Masa ‘Kiss’ Ya Girgiza Intanet

@I_Am_GeeBee ya tambaya:

"Wa zai ci dukkanin abincin da suka girka a wajen taron?"

Biki bidiri: An sha shagalin bikin wasu masoya da lemun kwalba biyu

A wani labari na daban, wasu ma'aurata sun tsuma zukatan mutane da dama sannan sun baiwa wasu mamaki kan yadda suka yi bikinsu a saukake.

Masoyan, wadanda ga dukkan alamu basu da wadatar aljihu, sun samu dandazon jama'a da suka halarci shagalin bikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng