'Yan Bindiga Sun Sace Ma'aikatan Titin Hanyar Kaduna-Kano
- Mahara da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun sace wasu daga cikin ma'aikatan da ke aikin titin hanyar Kaduna-Kano
- Ƴan bindigan dai sun farmaki ma'aikatan ne a gidansu da ke Tashar cikin ƙaramar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna
- A yayin harin ƴan bindigan sun yi awon gaba ɗa mutum huɗu daga cikin masu aikin yayin da wasu mutum biyu kuma suka samu raunika
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin da ke aikin titin hanyar Kaduna zuwa Kano a garin Tashar Yari na ƙaramar hukumar Maƙarfi a jihar Kaduna.
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa wasu daga cikin ma'aikatan mutum biyu sun samu raunika inda ake duba lafiyarsu a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke a Shika, Zaria.
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Dare a Arewacin Najeriya, Rayukan Mutane Da Yawa Sun Salwanta
Maharan dai sun kai harin ne a ranar Asabar.
Wata majiya a yankin ta bayyana cewa maharan sun yi wa gidan da ma'aikatan ke zaune ƙawanya ne sannan suka sace mutanen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Lamarin dai ya auku ne a babban titin Kaduna/Zaria/Kano wanda ma'aikatan na daga cikin masu yin aikin gyaran titin.
Majiyoyi sun tabbatar da aukuwar harin
Majiyoyi masu yawa da ke a garin Maƙarfi, ciki har da wani shugaban al'umma da baya son a ambaci sunansa sun tabbatar da aukuwar harin.
A cewar shugaban, maharan sun isa gidan ne da daddare lokacin ana ruwan sama, inda suka kai wa ma'aikatan hari ba tare da samun wata tangarɗa ba.
"An ɗauke mutum hudu, wasu mutum biyu kuma sun jikkata, waɗanda nan take aka garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu." A cewarsa.
Ƙoƙarin jin ta bakin jami'an ƴan sanda ya ci tura
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, DSP Mohammed Jalige, saboda rashin ɗaukar kiran wayar aka yi masa.
Sannan har lokacin kammala haɗa wannan rahoton bai dawo da saƙon da aka tura masa ta wayar salula ba.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Tara a Jihar Plateau
A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun kai wani sabon farmaki a ƙauyen Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
A yayin harin ƴan bindigan sun halaka mutun tare da ƙona wasu gidaje guda shida a ƙauyen kafin zuwan jami'an tsaro.
Asali: Legit.ng