Babban Kwamandan Boko Haram, Khaid Malam Ali, Ya Mika Wuya Ga Dakarun Sojojin Najeriya
- Kwamandan Boko Haram, Khaid Malam Ali, ya mika wuya ga dakarun rundunar sojojin Najeriya
- Malam Ali a ajiye makaman yakinsa tare da babban mayakinsa, Bunu Umar a jihar Borno
- Hakan na zuwa ne bayan yan ta'addan ISWAP sun murkushe mayakan Boko Haram masu yawan gaske a kusa da Bama
Borno - Wani babban kwamandan kungiyar ta'addanci na Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād wanda aka fi sani da Boko Haram, Khaid Malam Ali, ya mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya.
Malam Ali ya mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai da ke yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas tare da babban mayakinsa, Bunu Umar a jihar Borno, zagazola Makama, shahararren masanin lamarin tsaro a tafkin Chadi ya bayyana.
Yan ta'addan ISWAP sun fatattaki Malam Ali da mayakansa
An tattaro cewa ‘yan ta’addan ISWAP sun fatattaki Ali da mayakansa bayan sun kai wani shiryayyen hari maboyar Boko Haram a Bula Alhaji Garwaye a yankin Sambisa kusa da karamar hukumar Bama a ranar 5 ga Yuli, 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zagazola Makama ya rahoto yadda mayakan ISWAP suka kashe wasu mayakan Boko Haram masu yawan gaske da suka hada da mata da yara.
Ali ya kasance kwamandan yan ta'addan a Sabil Huda da Njumia. Ya ajiye makaman yakinsa saboda tsoron murkushe shi a filin Yaki.
Dakarun rundunar sojoji na ci gaba da aiki domin murkushe mayakan ta'addanci a yankin arewa maso gaba.
Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Filato
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindiga sun halaka mutum tara da ƙona gidaje shida a ƙauyen Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Mista Jerry Datim, ɗaya daga cikin shugabannin ƙauyen shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a birnin Jos ranar Lahadi.
Datim, wanda shine shugaban ƙungiyar Global Society for Middle Belt Heritage na ƙasa, ya bayyana cewa an kai harin ne a ranar Asabar da daddare.
"Jiya da daddare, ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen mu, Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Mangu, sun ƙona gidaje shida da lalata kayayyaki masu yawa."
Asali: Legit.ng