'Yan Sanda Sun Kama Wata Saniya Da ’Yan Kungiyar Asiri Suka Tanada Don Shagalinsu a Jihar Osun

'Yan Sanda Sun Kama Wata Saniya Da ’Yan Kungiyar Asiri Suka Tanada Don Shagalinsu a Jihar Osun

  • ‘Yan sanda sun kama wata saniya tare da tafiya da ita bayan kokarin kama wasu ‘yan kungiyar asiri a jihar Osun
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wasu ‘yan kungiyar asiri suka shirya yin wani katafaren biki a jihar
  • Ya uwa yanzu, ba a bayyana yadda hukumar ‘yan sanda ta yi da saniyar ba, amma an watsa ‘yan kungiyar

Jihar Osun - ‘Yan sanda a jihar Osun sun kama wata saniya da aka shirya yin amfani da ita a wajen bikin ranar ‘yan kungiyar asiri a Osogbo, babban birnin jihar, rahoton Vanguard.

Rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Alhamis ta yi gargadi game da bikin ‘Cult Day’ wanda kungiyar Aye ke gudanar da ita a duk ranar 7 ga watan Yuli, inda ta ce cewa za ta kama duk wanda ke da hannu wajen kawo taro ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA Tayi Kamen Masu Harkar Kwayoyi, An Yi Ram da Malaman Addini

Don tabbatar da bin doka da oda, rundunar ta fara sanya ido a duk fadin jihar tun ranar Juma'a tare da sintiri a yankuna daban-daban.

An kama saniyar tsafi a jihar Osun
Saniya, daya daga dabbobin gida da ake kiwonsu don nama da madara | Hoto: Dag Sundberg
Asali: Getty Images

‘Yan kungiyar asiri sun yi taronsu a wani yanki

Sai dai an tattaro cewa ’yan kungiyar asirin daga wurare daban-daban sun hallara a unguwar Egbatedo da ke babban birnin jihar domin bikin wannan rana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan yasa mazauna yankin suka sanar da jami’an ‘yan sandan da ke yaki da kungiyar asiri da suka mamaye yankin domin kama wadanda ake zargin ’yan kungiyar ne, The Whistler ta tattaro.

Wadanda ake zargin, bayan da suka ga jami’an ‘yan sanda sun tsere, inda suka yi bar saniyar, wadda tuni suka yi wa lakabi da “Orki Aye group, 7/7” da alamar gatari a jikin saniyar, wadda rundunar ‘yan sandan suka tafi da ita.

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya ce rundunar ‘yan sandan ta tafi da saniyar bayan wadanda ake zargin sun gudu.

Dan kungiyar asiri ya dana wa kansa harsashi a kokarin harba bindiga

A wani labarin, kun ji cewa, wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne ya harbi kansa a yayin da ya ke kokarin ciro masakar harsashi daga cikin wata bindiga kirar pistola a jihar Ogun.

Lindaikeji ta rahoto cewa Janai Sunday ya harbi kansa a hannu, a cewar hukumar tsaro ta Amotekun reshen jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.