Tashin Hankali Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Ekiti

Tashin Hankali Yayin Da Yan Bindiga Suka Sace Shugaban Jam'iyyar APC a Ekiti

  • Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Barista Paul Omotoso, shugaban jam'iyyar APC na jihar Ekiti
  • Rahotanni sun tabbatar cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a hanyar Agbado Ekiti zuwa Imesi Ekiti a jihar ta Ekiti
  • Segun Dipe, sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar Ekiti ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce jami'an tsaro na aiki don ceto shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti - An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na jihar Ekiti, Barista Paul Omotoso.

Daily Trust ta rahoto cewa an kai masa hari ne a ranar Asabar da yamma yayin da ya ke tuki a kan hanyar Agbado Ekiti - Imesi Ekiti.

An Sace Shugaban APC na Ekiti
Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban APC a Ekiti. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Sakataren watsa labarai na APC ya tabbatar da sace shugaban APC na jihar

Kara karanta wannan

Yadda APC Ta Hana Tinubu Kudi a Lokacin Kamfe In Ji Mataimakin Shugaban Jam’iyya

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a Ekiti, Segun Dipe, ya ce shugaban jam'iyyar yana tuka motarsa ne a hanyar a lokacin da abin ya faru, rahoton Leadership.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dipe ya ce:

"Shugaban jam'iyyar yana tuka motarsa kirar Venza ne a titin.
"Yan bindigan sun harbi daya cikin tayoyin motarsa. Aka dauke shi cikin wata mota Toyota Hilux aka tsere da shi. Shi kadai ne a cikin motar a lokacin da abin ya faru a cewar bayanin da muka samu.
"Abin ya faru da yamma, mun samu labari misalin karfe 6 na yamma. An sanar da jami'an tsaro - yan sanda da Amotekun, duk suna aiki a kan abin."

Wata kwakwarar majiya ta tabbatarwa Nigerian Tribune sace Omotosho tana mai cewa:

"Ciyaman din ya kira ni safiyar yau (Asabar) kuma mun yi magana mai tsawo kuma daga bayanin da muka samu, ya tafi ya ajiye direbansa ne kuma yana hanyar komawa garinsu shi kadai lokacin da masu garkuwa suka harbi motarsa suka fasa tayoyinsa.

Kara karanta wannan

An Ji Yadda Gwamnan PDP Ya Taimaki APC, Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

"Sun dauke shi daga wurin da abin ya faru kusa da hanyar Agbado - Imesi-Ekiti da motarsu zuwa wani daji kusa da Ise-Ekiti, wannan shine abin da na sani a yanzu.
"Gwamnan jihar, Biodunn Oyebanji ya san da abin da faruwar abin kuma ya dauki matakin gaggawa na kokarin ganin an sako ciyaman din."

Da aka tuntubi mai magana da yawun yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya ce a bashi lokaci idan ya tabbatar zai yi magana.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164