Mummunan Hatsarin Mota Ya Halaka Mutum Hudu a Birnin Tarayya Abuja
- Wata motar tirela ta bi ta kan wasu ababen hawa a birnin tarayya Abuja inda ta halaka mutum huɗu nan ta ke
- Motar tirelar wacce ta taho da gudu ta kasa tsayawa ne bayan burkinta ya ƙi ci wanda hakan ya sanya ta yi kan motocin
- Wasu mutane daban kuma sun samu munanan raunika a dalilin aukawar da motar tirelar ta yi wa ababen hawan
FCT, Abuja - Wani hatsari da ya ritsa da motar tirela ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutum huɗu a Dutse-Baupma kusa da gidan man AYM Shafa akan titin Dutse-Bwari a ƙaramar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.
Hatsarin wanda ya auku da tsakar rana a ranar Asabar, ya auku ne a dalilin ƙwacewar burkin motar tirelar wacce ta ɗebo yashi, cewar rahoton jaridar Leadership.
Hatsarin ya kuma ritsa da wata mota baƙa ƙirar Toyota Highlander Jeep, wata Hilux baƙa ta ƴan sanda da wata keke Napep.
Yadda hatsarin motar ya auku
Wani ganau ba jiyau ba, Abdul Mohammed, ya yi bayanin cewa burkin tirelar ya ƙwace ne a daidai kwanar Usman Dam akan babban titin Dutse-Bwari wanda hakan ya sanya ta faɗa kan ababen hawan inda kusan duk mutanen da ke cikinsu suka rasa ransu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Na kusa tsallakawa zuwa kan babban titin da motata lokacin da na hango tirelar ta taho da gudu ta wuce mu ta fara afkawa ababen hawa. Mutanen da ke a gefen garejin ƴan tifa sun yi sa'a da suka fahimci cewa motar ta ƙasa cin burki, sai suka yi ta kansu."
"Direban tirelar, fasinjojin da mutanen da ke cikin Hilux ɗin ƴan sandan nan ta ke suka riga mu gidan gaskiya, yayin da mutanen da ke a cikin Highlander ɗin da Keke Napep sun samu munanan raunika. Kusan mutum huɗu ne suka mutu nan ta ke."
"Wannan kwanar ta daɗe da zama kwanar mutuwa kuma babu abinda aka yi akai. Yakamata hukumomin birnin tarayya Abuja su kawo mana ɗauki anan wajen, yakamata su gayawa direbobin tireloli da su dai na bin wannan hanyar da rana sai da daddare."
A lokacin kammala haɗa wannan rahoton dai jami'an hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) sun tafi da gawarwakin waɗand suka rasun zuwa ɗakin ajiyar gawa, yayin da waɗanda suka samu raunika aka tafi da su zuwa asibiti domin basu agajin gaggawa.
Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Matafiya a Jihar Osun
A wani labarin na daban kuma, wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu matafiya a jihar Osun suna kan hamyarsu ta zuwa Arewacin Najeriya.
Rayukan aƙalla mutum biyu suka salwanta a hatsarin motan wanda ya auku akan titin hanyar Ife-Ondo.
Asali: Legit.ng