Kirkirar Sakamakon UTME: Innoson Ya Janye Tallafin Karatun Da Ya Baiwa Mmesoma

Kirkirar Sakamakon UTME: Innoson Ya Janye Tallafin Karatun Da Ya Baiwa Mmesoma

  • Kamfanin Innoson ya janye tallafin karatu da ya baiwa dalibar nan da ta kirkiri sakamakon jarrabawarta na UTME
  • Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Anambra ta kafa ya gano da gaske Joy Mmesoma Ejikeme ce ta kirkiri sakamakonta da ke dauke da maki 362
  • Sakamakon tabbatar da haka da binciken ya yi, kamfanin ya ce ya yanke hukunci mai wahala na hana dalibar tallafin karatu

Kamfanin motoci na Innoson ya janye tallafin karatu da ya baiwa Joy Mmesoma Ejikeme bayan kwamitin bincike na gwamnatin Anambra ya bayyana cewa sakamakon jarrabawarta na UTME na bogi ne, rahoton The Cable.

Kwamitin ya saki sakamakon bincikensa a ranar Juma'a, yana mai bayyana cewa Mmesoma ta yarda cewa ta kirkiri makin ta ne.

Kmafanin Innoson ya janye tallafin karatun da ya baiwa Mmesoma
Kirkirar Sakamakon UTME: Innoson Ya Janye Tallafin Karatun Da Ya Baiwa Mmesoma Hoto: @NTANewsNow/Charles Chukwuma Soludo
Asali: Facebook

Kamfanin motoci na Innoson ya janye tallafin karatun da ya baiwa Mmesoma

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Kwamitin Gwamnatin Anambra Ya Gano Bayan Binciken Sakamakon UTME Din Mmesoma Ejikeme Joy

PM News ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, Cornel Osigwe, shugaban sashin labarai na kamfanin motocin Innoson ya ce sun yanke shawara "mai wuya" na janye tallafin "a matsayin martani ga binciken da aka tabbatar".

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A yan kwanakin nan, mun kasance a cikin tsarin binciken zarge-zargen da ke kewaye da sakamakon jarrabawar UTME na 2023 na daya daga cikin wadanda suka ci moriyar shirinmu na bayar da tallafi, Miss Joy Mmesoma Ejikeme. da farko an rahoto cewa Miss Joy ta samu maki masu yawan gaske a jarrabawar, lamarin da ya kai ga kamfaninmu ya bata tallafin karatu," inji kamfanin.
"Sai dai kuma, rahotannin da suka biyo baya na rashin daidaito a makin da ta samu a jarrabawar UTME ya sa muka nemi karin haske daga hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) da kuma ba ta damar bayyana matsayinta, mun shiga tattaunawa kai tsaye da Miss Joy.

Kara karanta wannan

Ya Kamata a Bari Mmesoma Ta Samu Gurbin Karatu a Jami’a: Tsohon Ministan Buhari, Ya Fadi Dalili

“Bugu da kari, kwamitin da gwamnan jihar Anambra, Dr Charles Chukwuma Soludo ya kafa, ya gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin.
"A yanzu sakamakon binciken ya tabbatar da cewar Miss Joy Mmesoma Ejikeme ta yi kutse a sakamakon jarrabawarta na UTME. Wannan karshen na cike datakaici kuma ya sabawa ka'idodin da muke bi wajan dauka kamfaninmu na Innoson, musamman wadanda suka samu karancin maki a shirinmu na ba da tallafin karatu.
“Kamar yadda yake a wadannan ka'idoji namu da kuma martani ga binciken da aka tabbatar, mun yanke hukunci mai wahala na janye tallafin karatu da aka baiwa Miss Joy Mmesoma Ejikeme. Wannan aikinlamuni ne ga jajircewarmu ga gaskiya, rikon amana, da kuma cancanta."

Kamfanin ya kuma ce yana nan a kan bakarsa na tallawa daliban da suka cancanta da kuma zuba jari a bangaren ilimi na kasar.

Kwamitin bincike ya tabbatar da Mmesoma kirkiri makin 362 ne da kanta

Kara karanta wannan

Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB

Mun ji a baya cewa kwamitin binciken da gwamnatin jihar Anambra ta kafa ya tabbatar da cewa ɗalibar nan da ake zargi, Mmesoma Ejikeme, ta yi maguɗin sakamakon JAMB/UTME.

An tattaro cewa kwamitin, wanda gwamna Charles Soludo, ya kafa da nufin gano gaskiya, ya ce aihinin makin da ɗalibar ta ci shi ne 249 ba 362 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng