Mahajjaciyar Najeriya Ta Tsinci Miliyan 56 a Saudiyya, Ta Mayarwa Mai Shi

Mahajjaciyar Najeriya Ta Tsinci Miliyan 56 a Saudiyya, Ta Mayarwa Mai Shi

  • Wata yar Najeriya da ta sauke farali a kasar Saudiyya a bana ta kara daga darajar kasar da wani abun mamaki da ta aikata
  • Aishatu y’an Guru Nahuce ta tsinci tsabar kudi har dala 80,000 wanda ya yi daidai da naira miliyan 56 a garin Makkah
  • Sai dai kuma, ta mayar da kudin ga hukumar jin dadin alhazai ta jihar Zamfara ba tare da ta taba komai a ciki ba

Saudiyya - Wata mahajjaciyar Najeriya daga karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Aishatu y’an Guru Nahuce, ta tsinci kudi har dala 80,000 a kasar Saudiyya.

Hajiya Aishatu wacce Bafullatana ce bata yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da kudin wanda yawansu ya kai naira miliyan 56 a kudin Najeriya ga mahukunta.

Yar Najeriya ta tsinci kudi a Saudiyya amma ta mayar
Mahajjaciyar Najeriya Ta Tsinci Miliyan 56 a Kasar Saudiyya, Ta Mayarwa Mai Shi Hoto: @Abdool85
Asali: Twitter

Mahajjaciyar Najeriya ta mika miliyan 56 da ta tsinta ga hukumar jin dadin alhazai na Zamfara

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Allah Ya Yi Wa Matar Shahararran Dan Kasuwa, Dahiru Mangal, Rasuwa

Kamar yadda wani mai amfani da Twitter, Abdallah Yunus Abdallah (@Abdool85) ya wallafa a shafinsa a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, Hajiya Aisha ta mika kudin ne ga jami'an hukumar jin dadin alhazai ta jihar Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

"Wannan Bafulatanar matar mai suna Hajiya Aishatu y'an Guru Nahuce daga karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara ta tsinci kudi $80,000 (N56,000,000) a Makkah yayin aikin hajji sannan ta mika shi ga jami'an hukumar jin dadin alhazai ta jihar Zamfara."

Jama'a sun yi martani

@LimanTurawa jama'a ya yi martani:

"Kaji baiwar ALLAH..... ALLAH ya sa a gama lafiya "

@Dankalihu ya yi martani::

"Ma Shaaa Allah!!! “Allah Ubangijii Yasakha Matah Da Aljannatu Firdausi #Respect"

@ZuntuAbdullahi ya yi martani:

"Masha Allah."

@U_baba419 ya yi martani:

"Ace kaba ta rokon Allah ya yi maka abu sannan Allah ya baka nan take sai ka yanke shawarar bayar da shi ga wani."

Kara karanta wannan

Hana Sallar Juma'a: MURIC Ta Caccaki Gwamnan Jiha Kan Tauye Wa Musulmai Hakkin Yin Addini

Legit.ng ta tuntubi mawallafin labarin mai suna Ibrahim domin jin karin bayani daga gare shi amma bai amsa kiran waya ko sakonni da aka aika masa ta WhatsAPP ba.

Mijin jarumar Fim, Mercy Aigbe ya jinjina mata yayin da suka kammala aikin hajji

A wani labarin kuma, mun ji cewa jarumar Nollywood Mercy Aigbe ta yi godiya ga Allah madaukakin sarki da ya yi amfani da mijinta wajen kai ta aikin hajji a kasa mai tsarki.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, mijin jarumar mai suna Adekaz ya wallafa wani bidiyo inda jarumar ke nuna godiyarta ga Allah da ya yi amfani da shi wajen kai ta garin Makkah domin sauke farali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng