Sabuwar Amarya Ta Kai Karar Mijinta Kotu a Kaduna, Tana Son a Raba Aurensu Na Wata Hudu
- Wata sabuwar amarya ta kai ƙarar mijinta a gaban wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a jihar Ƙaduna
- Amaryar ɗai tana neman kotun da ta datse igiyar aurenta da mijinta inda ta aminve za ta mayar masa da kuɗin sadakin da ya biya
- Sai dai, mijin yana son matarsa inda ya buƙaci da ta ɗan ɗiɓar musu lokaci domin ya samu ya kawar da matsalar da ke a tsakaninsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Wata sabuwar amarya mai shekara 19 a duniya, Sumayya Muhammad, ta kai ƙarar mijinta a gaban kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, jihar Kaduna, domin a raba aurensu.
Matar auren wacce amarya ce tana neman kotu da ta datse igiyar aurenta na wata huɗu da Umar Ibrahim ta hanyar 'Khul'i', cewar rahoton jaridar Tribune.
Sumayya Muhammad ta hannun lauyanta ta bayyana cewa a shirye ta ke ta dawo da kuɗin sadaki har N100,000 da ta karɓa daga wajen mijinta domin ta fita daga cikin auren.
Ta kuma ƙara da cewa tana bin mijinta Umsr bashin kuɗi har N10,000 sannan ta roƙi kotu da ta taimaka mata wajen karɓo kuɗadenta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta bayyana cewa ba a samu rabo ba a tsakaninsu kawai ta ji yanzu ita sam ba ta ra'ayin ci gaba da zaman aure tsakaninta da mijinta.
"Ban ɗauke da juna biyu sannan bani da da ɗa. Kawai bana son ci gaba da auren." A cewarta.
Mijin yana son ci gaba da zama da matarsa
A nasa ɓangaren, wanda ake ƙarar ya bayyana cewa yana son matarsa inda ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci ya yi ƙoƙarin daidaita tsakaninsa da matarsa.
Ya yi bayanin cewa matarsa bashin N9,500 ta ke binsa ba N10,000 kamar yadda ta gayawa kotun.
Alƙalin kotun Malam Rilwanu Kyaudai ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar.
Amarya Ta Halaka Mijinta a Bauchi
A wani labarin na daban kuma, wata amarya a jihar Bauchi ta aikata aikin dana sani bayan ta kashe mijinta har lahira.
Amaryar mai kimanin shekara 21 a duniya mai suna Maimuna Sulaimam ta yi ajalin mijinta ne ta hanyar caka masa wuƙa wacce ta yi sanadiyyar rasuwarsa.
Asali: Legit.ng