Mmesoma: Dalibar Da Ta Hada Sakamakon JAMB Na Karya Ta Fadi Matakan da Ta Bi
- Ɗalibar Anambra ta ƙara bayani dalla-dalla kan hanyar da ta bi wajen ƙara yawan makin da ta ci a jarabawar JAMB 2023
- Ejikeme Joy Mmesoma ta shiga kanun labarai kusan mako ɗaya kenan ana kai kawo kan gaskiyar abinda ya haɗa ta da hukumar JAMB
- Da farko yarinyar ta yi ikirarin cewa maki 362 ta ci a JAMB amma bayan gaskiya ta yi halinta, da bakinta ta faɗi makircin da ta ƙulla
Anambra - Mmesoma Ejikeme, ɗalibar nan 'yar jihar Anambara da ta shiga kanun labarai a 'yan kwanakin nan, ta ƙara tabbatar da cewa ita da kanta ta kirkiri sakamakon jarabawar JAMB.
Da fari ɗalibar ta yi ikirarin cewa ta ci maki 362 a jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da Sakandire UTME wanda hukumar JAMB ke shirya wa.
Yayin da ake tsaka da taya ta murnar zama ɗaliba mafi kwazo, hukumar JAMB mai alhakin shirya jarabawar ta fito ta ce ƙarya ne sakamkon Mmesoma na gaskiya shi ne 249.
Rahoton kwamiti ya fayyace mai gaskiya tsakanin JAMB da Mmesoma
Bayan kusan mako ɗaya ana kai kawo kan wannan batu, daga karshe kwamitin binciken da gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya kafa ya fayyace gaskiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A rahoton kwamitin, ya ce Mmesoma Ejikeme ta amsa da bakinta cewa ita ta yi ƙulle-kullen jirkita makin da ta ci ya ƙara yawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Matakan da na bi na ƙara wa kaina makin JAMB - Mmesoma
Channels tv ta tattaro wani sashin rahoton kwamitin na cewa:
"A bayanin Ejikeme Joy Mmesoma a gaban shugaban makarantarsu da sakataren ilimi ta aminta cewa makin da hukumar JAMB ta faɗa da bayanin jami'anta shi ne gaskiyar abinda ya faru."
"Ƙaramar yarinyar ta kuma aminta cewa da hannunta ta ƙirƙiri sakamakon bogi ba tare da taimakon kowa ba, ta yi amfani lambar da ta yi rijistar JAMB mallakin kamfanin Airtel."
"A cewarta, bayan ta gama kirkira sai ta garzata shagon Cafe (Prisca Global Computers, Uruagu, Nnewi) ta ciro sakamakon da ta haɗa na bogi."
Kwamitin Bincike Ya Bayyana Abinda Yakamata Ya Faru Da Mmesoma Ejikeme Bayan Ta Kara Makin JAMB
A wani labarin na daban kuma Kwamitin da ya gudanar da bincike kan Kes din Mmesoma ya bada shawarwarin matakin da ya kamata a bi.
Kwamitin ya buƙaci Mmesoma Ejikeme da ta ba hukumar shirya jarabawar shiga jami'a (JAMB) haƙuri kan aika-aikar da ta tafka.
Asali: Legit.ng