Kundin Bajinta Na Guinness Ya Lamuncewa Dan Najeriya Yin Waka Na Awanni 200
- Wani dan Najeriya ya fara wakar yabo na awanni 200 a kokarinsa na shiga kundin tarihi na duniya
- Yayin da ya fara gasar a watan Yuli, mutumin ya bayyana cewa yana shirin kafa tarihi a matsayin mawaki ya fi kowa dadewa yana rera waka nan gaba kadan
- Bidiyon wajen da yake gasar wakar nasa a Lagas ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
Wani dan Najeriya mai suna Oluwatobi Kufeji Àlejòpàtàkì, ya fara rera wakar yabo da gasa a Lagas yayin da yake shirin shiga kundin tarihi na duniya a matsayin mawakin da ya fi kowa dadewa yana rera waka.
A ranar 10 ga watan Yuni, Oluwatobi ya wallafa a Instagram cewa kungiyar ta amince da bukatarsa na shafe tsawon awanni 200 yana rera waka sannan ya sanar da cewar zai kafa tarihi a matsayin mawaki mafi dadewa yana rera waka a nan gaba kadan.
Bidiyo: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Janareto Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara
Oluwatobi ya fara gasar wakar nasa a ranar 1 ga watan Yulin 2023 kuma tuni ya shafe sama da awanni 25 kamar yadda aka gani a wani bidiyo daga wajen taron wanda aka wallafa a shafinsa na Instagram.
Mutane sun taru a wajen yayin da suke kallon matashin a gasar da yake yi na rera wakar yabo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda yake a shafin yanar gizo na Kundin Bajinta Na Guinness, gasar waka mafi dadewa da wani ya yi ya shafe tsawon awanni 105 ne kuma Sunil Waghmare (India) ne ya yi a Nagpur kasar Indiya daga 3 zuwa 7 ga watan Maris din 2012.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@radianceaffair ta ce:
“Wai shin baku gaji da wannan shirmen na GWR ba! Kada ku ga laifin mutane idan suka ki fada maku hanyar da suka bi suka samu nasara a Najeriya, basa so aikinsu ya zama abun dariya. Abun akwai ban haushi a takaice.”
@dianejohn4luv ta ce:
“Wannan gasar kundin tarihi na duniya da kowa ke kokarin kafawa ya isa hujjar cewa mune muke yi wa kanmu a kasar nan…mune matsalar kanmu.”
@odcmedic ya ce:
“GWR sun siya sun tarar a Najeriya, za mu basu shaharar da basu taba tsammani ba, Ka sha waka yallabai…wanda ya fi kowa shiga karkashin ruwa ne kawai Najeriya ba za ta shafe ba saboda tuwo ya toshe makogwaronmu.”
Gwamnan Ekiti ya hana gasar kiss mafi dadewa a jihar don shiga kundin tarihi na duniya
A wani labarin, gwamnatin jihar Ekiti ta haramta gasar kiss na kwanaki uku da ake shirin yi wanda ake yi wa lakabi da “Kiss-a-Thon”.
Gasar wanda aka shirya farawa a ranar Juma'a, 7 ga watan Yuli, zai shafe tsawon kwanaki uku ana yinsa a jihar.
Asali: Legit.ng