"Zuma Ta Lulluɓe Jaririna Sa'o'i 24 Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Mahaifiyarsa a jihar Niger", Mahaifin Jariri

"Zuma Ta Lulluɓe Jaririna Sa'o'i 24 Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Mahaifiyarsa a jihar Niger", Mahaifin Jariri

  • Mahaifin jaririn da ƴan bindiga suka halaka mahafiyarsa ya bayyana yadda zuma ta lulluɓe jaririn kafin a ceto shi
  • Mallam Habibu ya bayyana cewa ƴan sakai sun samu jaririn lulluɓe da zuma a jikinsa lokacin da suka je ɗauko gawarwakin waɗanda aka halaka
  • Ya ce zumar ba ta yi wa jaririn komai ba inda yanzu haka yake a wajen yayar mahaifiyarsa wacce ke cigaba da shayar da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Niger - Mahaifin jaririn da aka ceto sa'o'i 24 bayan ƴan bindiga sun halaka mahaifiyarsa a jihar Niger, Mallam Habibu, ya bayyana yadda zuma ta lulluɓe ɗansa kafin ƴan sakai su ceto shi washe gari.

Ƴan bindigan dai sun halaka mahaifiyar jaririn ne, Sa'adatu Habibu, ana gobe Sallah a kwanar Maganda, kan titin hanyar Pandogari-Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Niger.

Kara karanta wannan

Da Sauran Rina: Abba Kyari Zai Cigaba Da Zama Gidan Yari Duk Da Samun Beli, Bayanai Sun Fito

Zuma ta lullube jariri har na sa'o'i 24 jihar Niger bayan 'yan bindiga sun halaka mahaifiyarsa
Jaririn da aka samu a raye Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Habibu ya gayawa jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa zuma ta lulluɓe yaron a gidan gaba na motar ƙirar Mitsubishi, inda mahaifiyarsa ta sanya shi kafin ta rasu, sannan an same shi ba tare da ciwo ba lokacin da ƴan sakai suka isa wajen.

Mahaifiyar jaririn ta sanya shi a gaban mota ƙafin ta rasu

Ya bayyana cewa matarsa da sauran mutanen da aka kashe a harin da an ceto su da ace akwai jami'an tsaro a yankin. Ya ƙara da cewa kafin ta rasu ta samu ta sauko da jaririn daga bayanta sannan ta sanya shi a gidan gaba na motar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mallam Habibu ya bayyana cewa matarsa tana dawowa ne daga Kontagora inda taje ziyarar mahaifinta, lokacin da ƴan bindigan suka tare hanyar suka halaka mutum shida da su ke tafiya a cikin motar ƙirar Mitsubishi.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Tinubu, Shugaban NPC Ya Yi Magana Kan Sabuwar Ranar da Za'a Yi Ƙidaya a Najeriya

A kalamansa:

"Jaririn yana goye a bayanta lokacin da suka harbeta, amma cikin sa'a harsashin bai same shi ba. Kafin ta rasu ta samu ta sauke shi daga bayanta ta aje shi a gidan gaba na motar."
"Ba nan da nan ta rasu ba, amma babu wanda zai iya zuwa wajen domin ya kai musu agaji. Babu kowa a wajen wanda zai taimaka musu ko ya kai su asibiti. Harin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma amma sai wajen ƙarfe 7:00 na yamma mu ka samu labari. Dare ya yi a lokacin domin ko ƴan sakai ba za su iya zuwa a wannan lokacin ba. Ba mu da abinda za mu iya yi."
"Lokacin da ƴan sakan suka je kwaso gawarwakin waɗanda suka rasu washe gari, an samu jaririn lulluɓe da zuma a jikinsa. Amma ba mu ga alamar rauni a jikinsa ba. An kawo shi gida da ransa sannan mu ka kai shi wajen likita domin a duba lafiyarsa. Yanzu haka yana wajen yayar mahaifiyarsa wacce ta ke shayar da shi."

Kara karanta wannan

"Babbar Kawata Za Ta Auri Mijina": Matar Aure Ta Koka Bayan Mijinta Ya Rabu Da Ita Saboda Ya Gama Lashe Albarkatunta

Habibu ya ce yana da wata matar amma an ba yayar mahaifiyarsa shi ne saboda tana da jaririn da ta ke shayarwa. Ya roƙi gwamnatin jihar Niger da masu bayar da agaji da su taimaka masa da abincin jariri da taimakon magani domin rainon jaririn.

Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga a Zamfara

A Wani labarin na daban kuma, dakarun sojoji sun halaka wasu miyagun ƴan bindiga mutum hudu a jihar Zamfara a yayin wani artabu da suka yi.

Dakarun sojojin sun kuma ceto wasu mutane da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su a yayin farmakin da suka kai maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng