Talauci da Jahilci Ne Suka Haddasa Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Sani Yerima
- Tsohon gwamnan Zamfara ya bayyana muhimman abu 2 da suka haifar da 'yan bindigan daji a arewacin Najeriya
- Sanata Ahmed Sani Yerima ya ce idan ka kalli duk masu hannu a lamarin, zaka ga talauci da jahilci ne suka jefa su ciki
- Ya kuma ƙara da cewa ko kaɗan ayyukan 'yan bindiga ba shi da alaƙa da albarkatun kasa da Allah ya azurta Zamfara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yerima, ya yi ikirarin cewa talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta'addancin 'yan bindigan jeji a Najeriya
A makon da ya gabata, Yerima ya buƙaci gwamnati ta rungumi tattaunawar sulhu da 'yan bindiga domin kawon karshen zubda jini, garkuwa da mutane da sauransu, Daily Trust ta tattaro.
Da yake hira da Channels tv cikin shirin Politics Today ranar Jumu'a, Yerima ya ce ingantaccen ilimi zai tsamo duk mai hannu daga aikata waɗan nan munanan ayyuka.
Yayin da aka tambaye shi kan abinda ya kawo matsalar 'yan bindiga, Yerima ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Babu wani mai ilimi, Musulmi ko kirista, Bayahude ko Hindu, wanda ke cikin hankalinsa kuma yana da aikin yi, bai haɗa hanya da talauci ba amma haka kurum ya ɗauki makami ya kashe mutane."
"Babbar matsalar da ta yi wa irin waɗan nan mutanen katutu ita ce talauci da kuma jahilci."
Gwamnatocin baya sun gaza kan batun yan bindiga - Yerima
Yerima, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya ƙara da cewa gwamnatocin baya ba su taɓuka komai ba wajen daƙile yaɗuwar yan bindiga.
"A baya gwamnatocin jihohi ba su kula da su ba, kuma ga barayin shanu sannan filin kiyon da aka ware musu duk manoma sun ƙwace," inji shi.
Tsohon gwamnan ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa ɗumbin albarkatun kasa da ke Zamfara kamar zinare na daga cikin manyan abubuwan da suka taka rawa wajen ƙaruwar ayyukan 'yan fashin daji.
Gwamnan Taraba Ya Ayyana Ilimin Firamare da Sakandire Kyauta a Jiharsa
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya maida ilimin makarantun Firamare da sakandire kyauta a jihar da ke Arewa maso Gabas.
Ya ce wannan na ɗaya daga cikin alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe, bayan haka zai rage raɗafin cire tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng