Bidiyon Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Shagalin Bikinsu Da Lemun Kwalba 2 Da Dan Karamin Kek Ya Ta Da Kura

Bidiyon Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Shagalin Bikinsu Da Lemun Kwalba 2 Da Dan Karamin Kek Ya Ta Da Kura

  • Wasu ma'aurata da suka yi shagalin bikinsu daidai ruwa daidai tsaki sun dauka hankalin jama'a a soshiyal midiya bayan bidiyon taron ya yadu
  • A yan baya-bayan nan ana ta samun karin mutane da ke yin aurensu a saukake amma na wadannan ma'aurata ya baiwa wasu da dama mamaki
  • A kan wani dan teburi da aka lullube a wajen taron, an gano lamun kwalba tare da wani dan karamin kek

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wasu ma'aurata sun tsuma zukatan mutane da dama sannan sun baiwa wasu mamaki kan yadda suka yi bikinsu a saukake.

Masoyan, wadanda ga dukkan alamu basu da wadatar aljihu, sun samu dandazon jama'a da suka halarci shagalin bikinsu.

An yi shagalin bikin a saukake
Bidiyon Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Shagalin Bikinsu Da Lemun Kwalba 2 Da Dan Karamin Kek Ya Ta Da Kura Hoto: @sutul02
Asali: TikTok

Sabanin yadda aka saba gani a wuraren biki, amaryar ta sanya tufafinta na yau da kullun sannan ta lullube kanta da wani mayani mai gani.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dan Najeriya Ya Baje Kolin Janareto Mara Amfani Da Fetur, Da Hasken Rana Yake Aiki Kuma Baya Kara

A daya bangaren, angon ya sanya kwat da wani dan kyakkyali a wuyansa. Yayin da limami ya jagoranci daurin auren kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya yadu a TikTok.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai dan karamin kek da lemun kwalba a kan teburinsu

Ma'auratan sun tsaya a gaban wani teburi da aka yi wa ado da dan karamin kek da kwalaben lemu. Daya an sha ya kai rabi.

Bidiyonsu ya ja hankalin mutane fiye da miliyan 4 da suka kalle shi. Sai dai kuma ba a tabbatar da wajen da aka yi daurin auren ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan bidiyon aure

user96681717329138 ya ce:

"Allah ya albarkace ku ya kuma daukaka ku. Allah ya sa ba za ku rasa komai ba. Ina maku addu'an soyayya da zaman lafiya a gidanku."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zubawa Ango Abinci Yayin da Take Kokarin Manna Masa ‘Kiss’ Ya Girgiza Intanet

Zandile Moyo410 ya ce:

"Allah ya albarkaci aurenku, na so wannan, ba wai zancen tara kyalkyal banza bane magana ce ta so."

Okwakoh ya ce:

"Toh yanzu yar'uwata za ki iya fada mani dalilin da ya sa har yanzu baki da aure kike yawo a gari."

zinnyb3 ta ce:

"Ah amma wa ya sha Pepsin ya kai rabi, ko daga kamfanin ne."

Susan 3070 ta ce:

"Na ga cewa babu wanda ke magana kan Pepsin da ya wuce rabi a kwalban."

Garin nuna zalama: Amarya ta yi wa ango barin abinci a jiki

A wani labari na daban, wata amarya ta yi wa angonta wankan abinci yayin da take kokarin burge mutane a wajen shagalin bikinsu.

Amaryar dai ta dare kan cinyar ango da nufin manna masa ‘kiss’ amma sai aka yi rashin dace abincin hannunta ya kife masa a riga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng