IPMAN Ta Lissafa Hanyoyi 4 Da Za a Bi Wajen Magance Tsadar Man Fetur a Najeriya

IPMAN Ta Lissafa Hanyoyi 4 Da Za a Bi Wajen Magance Tsadar Man Fetur a Najeriya

  • Kungiyar dilallan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana hanyoyi hudu da za a bi don kawar da tsadar man fetur a kasa
  • Mista Chinedu Anyaso, shugaban IPMAN na shiyyar Anambra, Ebonyi da Enugu ne ya bayyana haka a Awka babban birnin jihar Anambra
  • Ya kuma bayyana cewa karin farashin mai da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur ya shafi cinikin da ‘yan kasuwar man ke yi

Awka, jihar Anambra - Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana cewa tace man fetur a cikin gida ne babbar hanyar karya farashinsa a kasuwa.

Shugaban IPMAN na shiyyar Anambra, Ebonyi da Enugu, Mista Chinedu Anyaso ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Awka ranar Juma’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Abin da Ya Gagari Buhari, Ya Sasanta Rikicin Hukumomi 2 a Cikin Wata 1

IPMAN ta zayyano hanyoyin magance tsadar fetur a Najeriya
IPMAN ta lissafo hanyoyi 4 da za a bi don magance tsadar man fetur a Najeriya. Hoto: TVC News
Asali: UGC

Tsadar man fetur ta shafi cinikin da ‘yan kasuwar mai ke yi

Ya ce karin farashin na man fetur da aka samu sakamakon janye tallafi ya shafi har ‘yan kasuwa saboda an samu raguwar bukatar man.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ya yaba da kaddamar da matatar man Dangote da aka yi a kwanakin baya bayan nan tare da bayyana fatan cewa za ta fara aiki da wuri-wuri.

A cewarsa, hanyar da za a magance tashin farashin da ake samu na man fetur shi ne a fara samar da shi a cikin gida.

Hanyoyi hudu da za a bi wajen magance tsadar farashin man fetur a Najeriya

Mista Chinedu ya lissafo hanyoyi hudu da za a bi domin tabbatar da samun saukin farashin man fetur kamar haka:

1. Gyara matatun man Najeriya guda hudu da ake da su

Kara karanta wannan

Har An Fara Murna, Sai AA Rano Ya Musanta Karya Farashin Litar Fetur Daga N540

2. Fara aiki a matatar man Dangote cikin gaggawa

3. Gina karin wasu matatun man don gamsar da bukatuwar cikin gida

4. Ba da lasisi ga karin ‘yan kasuwa wajen harkokin na man fetur

Anyaso ya kuma kara da cewa, matatun man na cikin gida za su taimaka wajen sauke farashin wasu kayayyakin irinsu gas, kalanzir, da iskar gas saboda ba za a bukaci kudaden waje ba wajen hada-hadarsu.

Peoples Gazette ta ruwaito cewa, yanzu haka ana siyar da man fetur din kan N540 zuwa N550 a duk lita a Awka jihar Anambra.

IPMAN ta ce babu shirin tada farashin man fetur daga yadda yake a yanzu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa kungiyar IPMAN ta karyata rade-radin da ake na cewa farashin man fetur zai karu cikin ‘yan kwanakin nan.

Shugaban IPMAN, reshen shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Dele Tajuddeen ne ya bayyana hakan a Ibadan jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng