Lokuta 5 Da Hukumar JAMB Ta Kama Daliban Da Suka Buga Sakamakon Jarabawa Na Bogi
A cikin ‘yan kwanakinnan ne dai ake ta musayar yawu tsakanin hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB), da wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme ‘yar asalin jihar Anambra.
Mmesoma ta bayyana cewa ta samu maki 362 cikin 400 a jarabawar JAMB da ta rubuta.
Sakamakon jarabawar na ta ya dauki hankula sosai, musamman ma a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya sanya Mmesoma ta samu kyaututtuka da alkawura da dama daga mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnatin jihar Anambra ta nemi hukumar JAMB ta binciko gaskiyar sakamakon Mmesoma
Gwamnatin jihar Anambra ta yi matukar farinciki da sakamakon, sai dai ta nemi hukumar jarabawar ta JAMB, ta tabbatar ma ta da sahihancin sakamakon.
An samu akasi, yayin da JAMB ta bayyana cewa sakamakon Mmesoma ba gaskiya ba ne bogi ne, kuma ainihin abinda ta ci a jarabawar shi ne 249 ba 362 ba.
Hukumar ta JAMB ta dauki tsattsauran mataki kan Mmesoma, ta hanyar dakatar da ita daga sake rubuta jarabawar na tsawon shekara uku.
Mutanen da hukumar JAMB ta samu da laifin buga sakamakon bogi a shekarun baya
A yayin da ake ci gaba da tafka muhawara game da batun jarabawar wannan daliba ‘yar jihar Anambra, Legit.ng ta tattaro muku karin wasu daliban da JAMB ta kama da laifin buga sakamako na bogi a baya daga shafin Premium Times.
1. A shekarar 2021, an samu wani dalibi mai suna Ifesinachi John dan shekara 19, da ya yi ikirarin cewa 380 ya ci a jarabawar ta JAMB.
Sai dai hukumar ta JAMB bayan gudanar da bincike, ta gano karya yake yi, inda har ta kai ga hukumar ta hannanta shi ga ‘yan sanda kamar yadda jaridar This Day ta wallafa.
2. A shekarar 2019, JAMB ta titsiye wani matashi Kingsley Unekwe mai shekaru 18, wanda ya yi ikirarin kara yawan sakamakon da ya samu daga 201 zuwa 269.
Sai dai hukumar ta JAMB ta bayyanawa jama’a cewa akwai irin wadannan daliban da suka bugo sakamako na bogi da yawa, wanda wasu ‘yan damfara ke hada musu
3. Har ila yau, a wannan shekarar ta 2019 din dai, JAMB ta kama wani matashi Adah Eche mai shekaru 19 da laifin sauya sakamakonsa daga 153 zuwa 290, inda daga bisani ya turawa hukumar sako cewa sun yi kuskure a sakamakonsa.
Bayan gudanar da bincike, JAMB a gano cewa wasu ‘yan damfara ne suka bugawa matashin sakamakon bogi kamar yadda Nigerian Tribune ta kawo.
4. A wannan shekarar dai ta 2019, JAMB ta zargi wani mai suna Cletus Kokowa da canja sakamakon jarabawarsa daga 162 zuwa 206, wanda y ace ya biya wasu ‘yan damfara N10,000 don su yi masa.
5. JAMB ta sake zargin wata dalibar mai suna Rejoice Mordi yar shekara 19, da sauya sakamakon jarabawarta daga 164 zuwa 264.
Rejoice ta shaidawa JAMB cewa ta samu sakamakon jarabawar na bogi ne daga wurin wani mai suna Iyanu Oluwa ta Whatsapp.
Dalibar da ake zargi da magudin jarabawar JAMB ta fadi sakamakonta na gaskiya
Legit.ng a baya ta kawo muku cewa dalibar da ake zargi da kawo sakamakon jarabawar JAMB na bogi, daga baya ta bayyana ainihin abinda ta samu.
Mmesoma Ejikeme ta bayyana cewa 249 ne ainihin abinda ta ci a jarabawar ta JAMB da ta rubuta ta shekarar 2023.
Asali: Legit.ng